Liverpool ta huce a kan Bournemouth ta hau kan teburin Premier

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta doke Bournemouth 3-0 a wasan mako na biyar a Premier League da suka kara a Anfield ranar Asabar.
Luis Díaz ne ya ci wa Liverpool ƙwallon farko, sannan ya kara na biyu a minti biyu tsakani daga nan Dawin Nunuz ya ci na uku, kuma duk kafin hutu.
A wasan mako na huɗu ne a Premier League League, Liverpoo; ta ci karo da koma baya, inda Nottingham Forest ta doke ta 1-0 a Anfield.
Wannan nasarar da Liverpoo; ta samu ranar Asabar ya sa ta koma ta farko a kan teburi da maki 12, bayan wasa uku.
ai dai makin ya zama iri ɗaya da na Aston Villa mai wasa biyar da na Manchester City mai karawa huɗu, wadda za ta fuskanci Arsenal ranar Lahadi a Etihad.
Tun kan wannan wasan Bournemouth ba ta doke Liverpool ba a Anfield, wadda ta yi rashin nasara tara daga wasa 10 kafin ranar Asabar.
Mohamed Salah bai samu damar cin ƙwallo ba a karawar, wanda ya ci Bournemouth karo tara a baya.
A kakar bara sau uku Liverpool ta do ke Bournemoth har da 4-0 da ta yi rashin nasara a gida a Premier da fitar da ita da aka yi a League Cup 2-1.
A makon jiya Liverpool ta je ta doke AC Milan 3-1 a wasan farko a Champions League a Italiya. na kakar nan.
Ranar Laraba 25 ga watan Satumba, Liverpool za ta kara da West Ham a League Cup daga nan ta je Wolverhampton a Premier League ranar Asabar 28 ga watan Satumba.











