Za a yi bincike kan ɗaliba ƴar TikTok da ta ci kwalar malamin jami'a

...

Asalin hoton, Nnamdi Azikiwe University

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Jami'ar Nnamdi Azikwe ta ce za ta gudanar da bincike kan wani lamari da ya faru, inda aka ga ɗaliba ta ci kwalar wani malamin jami'ar.

A cikin sanarwar da aka fitar, mai magana da yawun jami'ar, Njelita Loius ta ce jami'ar ta ɗauki wannan lamari da matuƙar muhimmanci, sannan ta buƙaci duk waɗanda abin ya shafa su kwantar da hankalinsu.

A cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga ɗalibar ta far wa malamin jami'ar, Dr Chukwudi Okoye, bayan ya ratsa ta cikin bidiyon da take ɗauka a wani lungu da ke harabar jami'ar.

Lamarin dai ya faru ne a ranar 11 ga watan Fabarairu a jami'ar ta Nnamdi Azikwe da ke garin Awka na jihar Anambra, kudu maso gabashin Najeriya.

Rikici tsakanin mutanen biyu ya ɓarke ne a lokacin da Dr Okoye ya taɓi kafaɗar ɗalibar a lokacin da take ɗaukar bidiyon TikTok, tare da cewa 'ba ni wuri' yayin da yake gittawa ta baya.

Daga nan ne matashiyar ta dakata, sannan ta kalli malamin ta ce "jibi yadda ya buge ni".

Daga nan ne ake zargin ɗalibar ta far wa malamin kan lamarin.

Bidiyon ya nuna yadda ɗalibar ta kama malamin da faɗa har ta yaga masa wani ɓangare na riga jamfa da yake sanye da ita.

Ta riƙe malamin kamkam, sai dai malamin jami'ar ya kasance cikin yanayi na natsuwa, ba tare da wani yunƙuri na mayar da martani ba, har ƙarshen bidiyon.

Jami'ar ta Nnamdi Azikwe ta ce za ta ɗauki mataki gwargwadon sakamakon da bincike ya nuna.

"Bisa tsarinmu na tabbatar da ɗa'a da dogaro da kai da kuma yin komai kan tsari, da kuma ƙoƙarinmu na tabbatar da adalci, mai riƙon muƙamin shugaban jami'ar, Joseph I. Ikechebelu, ya umarci a gudanar da cikakken bincike na adalci da rashin nuna son rai kan lamarin," in ji sanarwar.

Bayanai daga jami'ar sun nuna cewa ɗalibar tana karatu ne a sashen tarihi da nazarin hulɗar ƙasashen duniya, a shekara ta uku.

Duk da cewa hukumomin jami'ar ba su sanar da tsawon lokacin da za a kwashe ana binciken ba, amma sun ce za su riƙa bayar da bayanai lokaci zuwa lokaci.