Barca da Real za su yi wasan karshe na takwas a Copa del Rey

Asalin hoton, Getty Images
Birnin Sevilla ne zai karɓi bakuncin El Clasico a wasan karshe a Copa del Rey tsakanin Barcelona da Real Madrid ranar Asabar.
Za a fafata ne a filin wasa na La Cartuja, kuma karo na takwas da za su kece raini a wasan karshe a Copa del Rey a tarihi.
Real ce kan gaba da yin nasara huɗu a kan Barcelona daga wasa bakwai baya, har da wanda ta lashe a 2011 da kuma 2014 da ba za ta manta da bajintar da ta yi ba.
A shekarar 2011, Real Madrid ta ɗauki Copa del Rey karkashin Jose Mourinho, bayan kaka 18 rabon ta da kofin.
Ƙungiyar Santiago Bernabeu ta ci 1-0 ta hannun Cristiano Ronaldo a wasan a karin lokaci, inda Pep Guardiola ne ya ja ragamar Barcelona.
Shekara uku tsakani, manyan ƙungiyoyin Sifaniya sun kara haɗuwa a wasan karshe a Copa del Rey a Valencia - Real ce ta yi nasarar cin 2-1.
A wasan ne Gareth Bale ya ci wata ƙwallo mai kayatarwa daga yadi na 50, karkashin Carlo Ancelotti, yayin da Angel Di Maria ne ya fara ci wa Real Madrid ƙwallon.
Haka kuma Real ta lashe Copa del Rey a kan Barcelona a 1975, ita kuwa Barcelona ta ɗauki kofin a kan Real Madrid a 1968 da 1983 da kuma 1990.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A kakar nan ta 2024/25 Barcelona ta yi nasara biyu a kan Real Madrid, bayan da ta je ta ɗura 4-0 a La Liga a Santiago Bernabeu cikin watan Oktoba.
Haka kuma Barcelona ta lashe Spanish Super Cup na bana, sakamakon doke Real Madrid 5-2 a wasan karshe a Saudiyya a cikin watan Janairu.
A wasan na hamayya da za a yi ranar Asabar, Barcelona na sa ran lashe Copa del Rey na 31, Athletic Bibao 24 ne da ita, sai Real Madrid ta uku mai 20 a jimilla.
Barcelona da Real Madrid sun haɗu a wasan karshe a gasar kofi sau 18, amma ba su taɓa haɗuwa ba a wasan karshe na Champions League a tarihi.
Cikin wasa 18 a wasan karshe da suka kara, Real ta lashe kofi 11 daga ciki Copa del Rey guda huɗu da Spanish Super Cup bakwai.
Ita kuwa Barcelona ta ɗauki kofi bakwai a kan Real Madrid ciki har da Copa del Rey uku da Spanish Super Cup uku da Spanish League Cup a 1983.
Ƴan ƙwallon Barcelona da za su fuskanci Real Madrid:
Ter Stegen, Cubarsí, R. Araujo, I. Martinez, Gavi, Ferran, Pedri, Ansu Fati, Raphinha, Iñaki Peña, Pablo Torre da kuma Christensen.
Sauran sun haɗa da Fermín, Pau Víctor, Lamine Yamal, Olmo, F. De Jong, Kounde, Eric, Szczęsny, H. Fort da kuma Gerard Martín.
Ƴan wasan Real Madrid da za su kara da Barcelona:
Masu tsare raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.
Masu tsare baya: Alaba, Lucas V., Vallejo, Fran García, Rüdiger, Mendy da kuma Asencio.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler da kuma Ceballos.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick da kuma Brahim.










