Valverde ya buga wa Real Madrid wasa na 150 ranar Lahadi

Fede Valverde

Asalin hoton, Real Madrid FC

An wallafa

Ranar Lahadi Real Madrid ta je ta doke UD Almeria da ci 2-1 a wasan makon farko a gasar La Liga kakar 2022/23.

Fede Valverde ya buga wa Real Madrid fafatawar, kuma karo na 150 da ya yi kenan a kungiyar ta Santiago Bernabeu.

Kaka ta biyar kenan da dan kwallon tawagar Uruguay ke taka leda a Real Madrid, wanda aka yi nasara da shi a wasa 98 ya kuma ci kwallo shida .

A kakar da ta wuce ta 2021/22 ita ce Valverde yafi taka rawar gani, wanda ya buga karawa 46 aka yi nasara da shi a wasa 32.

Bayan kammala kakar bara, Real Madrid ta lashe Spanish Super Cup da La Liga da kuma Champions League.

Ranar Laraba Valverde ya fara daga UEFA Super Cup, kuma kofi na bakwai jumulla da ya dauka a Real Madrid kawo yanzu.

Kofunan sun hada da Champions League da Club World Cup da UEFA Super Cup da LaLiga biyu da kuma Spanish Super Cup biyu.