Raunin da Martinez ya ji mai muni ne - Ten Hag

Asalin hoton, Getty Images
Kociyan Manchester United, Erik ten Hag ya ce raunin da Lisandro Martinez ya ji mai muni ne bai da ƙyaun gani.
Mai tsaron bayan ya riƙe ƙafarsa yana sharɓar kuka lokacin da ya ji ciwo a wasan Premier League da United ta ci West Ham 3-0 ranar Lahadi.
Wasa na uku da Martinez ya buga kenan a Premier League, bayan da ya daɗe yana jinya.
Ten Hag ya ce ya damu da raunin da mai tsaron bayan ya ji, kuma zai zamar masa koma baya a kakar nan.
Martinez ya ji rauni a zagaye na biyu, bayan da ya yi ƙoƙarin tare ƙwallo daga wajen mai tsaron bayan West Ham, Vladimir Coufal.
Ɗan ƙasar Argentina ya buga wasa na uku a United a lik, bayan sama da wata uku da ya yi jinyar rauni a ƙafa.
Wasa 22 ne Martinez bai buga ba, sakamakon jinya, wanda ya samu komawa taka leda a karawar da United ta yi da Tottenham ranar 14 ga watan Janairu.
Ranar Lahadi United ta doke West Ham 3-0 a wasan mako na 23, hakan ya sa ta koma mataki na shida a kan teburi da maki 38.
United za ta kara a wasan mako na 24 a Premier League ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairu, inda za ta ziyarci Aston Villa a Villa Park.
A kuma ranar ce West Ham za ta karɓi baƙuncin Arsenal a wasan hamayya tsakanin ƙungiyoyin Landan a babbar gasar tamaula ta Ingila.












