Za a iya dakatar da Rudiger tsawon lokaci bayan jifan alkalin wasa da ƙanƙara

Antonio Rudiger

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Antonio Rudiger na fuskantar barazanar dakatarwa daga buga wasanni bayan da alkalin wasa ya ba shi jan kati a wasan karshe na Copa del Rey.

Real Madrid ta sha kashi a hannun Barcelona da ci 3-2 a wasan da aka buga a filin wasa na Seville.

Rudiger da Lucas Vasquez sun samu jan kati a wasan duk da cewa an sauya su, saboda nuna fushi da suka yi kan rashin hura wa Mbappe keta da aka yi masa, jim kaɗan kafin a tashi a wasan.

Har ila yau, an sallami Jude Bellingham daga bisani - saboda nuna rashin ɗa'a.

Alkalin wasa Ricardo de Burgos Bengoetxea ya rubuta a rahotonsa cewa an kori Rudiger ne "saboda jifa na da wani abu - ƙanƙara - wanda bai same ni ba".

Ɗan wasan na iya fuskantar dakatarwa na tsawon lokaci, kamar yadda dokokin hukumar kwallon kafa ta Sifaniya suka tanadar ga wanda ya yi irin laifin.

''Idan aka duba sashi na 104 na dokar, wanda ya bayyana cewa idan aka ci mutuncin alkalin wasa - hukuncinsa shi ne dakatarwa na watanni uku zuwa shida - idan har bai yi wa alkalin wasa lahani ba," a cewar RFEF.

Sai dai ɗan wasan ya fito ya ba da hakuri kan lamarin a shafinsa na sada zumunta a yau Lahadi.