Abin da muka sani kan harin da Isra'ila ta kai wa Iran

Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta kai abin da ta kira ''harin da ta tsara'', ta sama kan Iran a wani martani kan hare-haren makamai masu linzami da Tehran ta ƙaddamar kan Isra'ilar a farkon wannan wata.
Shi ne hari na baya-bayan nan a musayar wuta tsakanin ƙasashen biyu na tsawon watanni da ya haifar da ɓarkewar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.
Yayin da rahotonni farko ke cewa hare-haren ba su kai yadda ake tsammani ba, a ranar Asabar Iran ta ce hare-haren kan sansanonin sojinta ya kashe dakarunta huɗu.
Ga abin da muka sani game da hare-haren.
Ta yaya hare-haren suka faru?
Da misalin karfe 02:15 na daren agogon Tehar (a ranar Juma'a), kafofin yaɗa labaran Iran suka bayar da rahoton samun fashewar wasu abubuwa a ciki da wajen Tehran babban birnin ƙasar.
Bidiyon da aka ɗora a shafukan sada zumunta, waɗanda BBC ta tantance, sun nuna yadda makaman ke shawagi a sararin samaniyar birnin, yayin da mazauna wasu yankunan suka ba da rahoton jin ƙarar hayaniya.
Jim kaɗan bayan haka, Rundunar Sojinn Isra'ila (IDF) ta tabbatar da kai hare-hare kan wuraren da ta ''tsara'' a ''sansanonin sojin'' Iran.
Hare-haren da aka kai da jiragen sama, ciki har da jirage marasa matuƙa. Wuraren da aka kai wa harehraen sun haɗa da sansanin sohohin saman ƙasar, da cibiyar ƙera makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa, da inda ake harba makamai a ƙasar.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ministan tsaro Yoav Gallant ya bibiyi hare-haren daga cibiyar kula da rundunar IDF a birnin Tel Aviv.
An yi ta kai hare-haren ta sama, har na tsawon sa'o'i uku. Kuma bayan kusan ƙarsfe 06:30 na safe, IDF ta ce an kammala hare-haren.
Fadar White House ta bayyana hare-haren a matsayin "aikin kare kai". Wani babban jami'in gwamnati ya ce Amurka ta yi aiki tare da Isra'ila don ƙarfafa mayar da martani kan "wasu wuaren da ka yi niyya".
Yaya girman hare-haren?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kawo ba a san girma da irin ɓarnar da hare-haren suka yi ba.
Rundunar Sojin Isr'ila ta ce hare-haren sun faɗa kan wurare 20 da ta nufata, ciki har da wuraren ƙera makamai masu linzami da wurin harba makaman da sauran sansanonin sojin ƙasar.
Rundunar sojin Iran ta tabbatar da mutuwar sojojinta huɗu yayin da biyu ke ''jinya raunukan da suka samu''.
Hukumomin Iran sun ce hare-haren sun faɗa a lardunan Khuzestan da Ilam da ke birnin Tehran.
Hukumar tsaron sararin samaniyar ƙasar ta ce, ta samu ''nasarar kakkaɓo'' wasu hare-haren, amma ''wasu wuraren ɓarnar da aka samu taƙaitacciya ce''.
Sashen tantance labarai na BBC ya gano wata ɓarna a shalkwatar tsaron ƙasar da ke gabashin birnin Tehran, da kuma a sansanin sojin sama da ke kudancin birnin.
Wani babban jami'i a gwamnatin Amurka ya ce hare-haren ba su lalata rijiyoyin man Iran ko tashar nukiliyarta ba, wuraren da shugaban Amurka Joe Biden ya yi gargaɗin kai wa hari.
Can ma a Siriya, kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito samun hare-hare a sansanin sojin ƙasar a tsakiya da kudancin ƙasar, kodayake Isra'ila ba ta tabbatar da kai hari cikin ƙasar ba.
Me ya sa Isra'ila ta kai wa Iran hari?
Iran ce ƙasar da ke goyon bayan ƙungiyoyi daban-daban a Gabas ta Tsakiya, waɗanda galibi ke adawa da Isra'ila, ciki har da Hamas da Hizbullah, da a yanzu haka Isra'ila ke yaƙi da su.
A cikin watan Afrilu, Iran ta ƙaddamar da harinta na farko kai tsaye kan Isra'ila, da kusan makamai masu linzami 300 da jirage marasa matuƙa, a matsayin ramuwar gayya kan harin da Isra'ila ta kai a harabar ofishin jakadancin Iran a Syria, wanda ya kashe wasu manyan kwamandojin dakarun juyin juya hali na Iran (IRGC).
Isra'ila ta mayar da martani da wani hari da ta ''ƙayyade" kan cibiyar tsaron makamai masu linzami a yankin Isfahan na Iran, wanda Iran ɗin ta ƙi mayar da martani.
Daga baya, a cikin watan Yuli, Isra'ila ta kashe wani babban kwamandan ƙungiyar Hizbullah a wani hari da ta kai ta sama a Beirut.
Washegari kuma, aka kashe shugaban siyasar Hamas Ismail Haniyeh a wani fashewa da aka yi a Tehran. Iran ta zargi Isra'ila, kodayake Isra'ila ba ta ce komai ba.
A ƙarshen watan Satumba, Isra'ila ta kashe shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah da kuma Birgediya-Janar Abbas Nilforoushan, wani babban jami'in Iran a Beirut.
A ranar 1 ga watan Oktoba ne Iran ta harba makami mai linzami kusan 180 kan Isra'ila, wanda ta ce martani ne kan kisan Haniyyah da Nasrallah da Nilforoushan.
Lamarin da ya sa ta mayar da martani a wannan hari na baya-bayan nan.
Me zai faru a gaba?
Firaministan Isra'ila benjamin Netanyahu ya musanta wani rahoto da kafar yaɗa labaran Axios ta Amurka ta yi cewa gabanin harin Isra'ila ta aike wa Iran saƙo tare da bayyana mata cikakken bayani game da hare-haren, tare da gargaɗin Iran kada ta mayar da martani.
"Isra'ila ba ta sanar da Iran kafin hare-haren ba, balle lokacin da za a kai su da kuma inda za a kai su da irin makaman da za a yi amfani da su,'' in ji kakakin Natenyahu.
Haka kuma, bayanan farko sun nuna cewa harin bai yi munin da ake fargaba tun da farko ba.
A cikin wat sanarwar rundunar sojin Isra'ila ta ce ''mun mayar da hankali kan burinmu na yaƙi a Gaza da Lebanon. Iran ce ke ƙoƙarin faɗaɗa yaƙin zuwa na yanki''.
Wani babban jami'in Amurka ya ce '' wannan ka iya kawo ƙarshen musayar wuta kai-tsaye tsakanin Isra'ila da Iran''.
Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce ''ƙasar na da damar kare kanta'' sanna ya bayyana hare-hare saɓa wa dokokin duniya.
Amma kuma ta ce Tehran ta fahimci ''gudunmowarta wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron yankin gabas ta tsakiya''.
Wane yanayi ake ciki a Iran?
Hotunan da kafafen yada labaran Iran suka wallafa sun nuna yadda rayuwa ke ci gaba da gudana cikin kwanciyar hankali - tare da cunkoson tituna, mutane suna motsa jiki a wuraren shaƙatawa, kasuwannin 'ya'yan itace da kayan lambu na ci gaba da hada-hada kamar yadda aka saba.
Iran ta rufe sararin samaniyarta na 'yan sa'o'i cikin daren, amma daga baya ta buɗe, kuma jiragen ɗaukar fasinja sun ci gaba da zirga-zirga faɗin ƙasar.
Sai dai akwai alamun gwamnatin Iran na son yin watsi da tasirin hare-haren.
Rundunar juyin juya halin ƙasar ta IRGC ta sanar da cewa laifi ne wallafa “hotuna ko labarai” masu alaƙa da harin zuwa shafukan yanar gizo da take ganin suna da alaƙa da Isra’ila ko kuma ‘yan adawa.
Kafofin yada labaran Iran sun ruwaito cewa ofishin mai shigar da ƙara na Tehran ya shigar da ƙara a kan wani gidan yanar gizo da ba a bayyana sunansa ba saboda "rufe batutuwan da suka shafi tsaron kasa".
Yaya duniya ta mayar da martani?
Kakakin Majalisar Tsaron Amurka Sean Savett ya ce martanin da Isra'ila ta mayar "ya kauce wa wuraren da jama'a suke, kuma sun mayar da hankali ne kawai kan sansanonin soji, saɓanin harin da Iran ta kai kan Isra'ila wanda ya auna birni mafi yawan jama'a na Isra'ila".
Amma manufar Amurka, a cewarsa "hanyar diflomasiyya don magance tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya".
Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer ya ce Isra'ila na da 'yancin kare kanta, amma ya buƙaci duka ɓangarorin su "nuna haƙuri", sannan ya yi kira ga Iran kada ta mayar da martani.
Saudiyya ta yi Allah wadai da harin, tare da gargaɗi kan duk wani mataki da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin.
Ma'aikatar harkokin wajen Masar ta yi na'am dadamuwar Saudiyyar, tana mai cewa "ta damu matuƙa" da hare-haren.
Kungiyar Hamas ta bayyana su a matsayin keta mutuncin Iran, kuma hakan zai haifar da barazana ga tsaro da zaman lafiyar mutanen yankin Gabas ta Tsakiya''.











