Tsadar gas da kalanzir ta sa yan Najeriya yin girki da gawayi

Charcoal
An wallafa

Tsadar rayuwa na kara zama wani babban kalabule ga talakawan Najeriya.

Baya ga tashin farashin man fetur da iskar gas da kuma kalanzir, farashin abinci na ci gaba da hauhawa, wanda wani al'amari ne da aka dade ba a ga irinsa ba a kasar.

Tashin farashin gas da kalanzir ya sa 'yan Najeriya da dama sun koma amfani da gawayi  domin yin girki.

Wani magidanci ya shaida wa BBC cewa tsadar gas ce ta sa shi ya hakura ya koma amfani da gawayi.

“Tun muna sayen gas a kan naira dubu daya da dari shida, ya koma dubu biyu da dari biyar har ya haura ya koma dubu hudu da dari biyar, yanzu kuma ya haura dubu hudu da dari takwas”, in ji shi.

Sai dai yawan bukatar da ake yi wa gawayin ta sa farashinsa ya tashi a kasuwa.

Ismaila Abubakar, mai sayar da gawayi ne a kasuwar Taurani da ke Kano, kuma ya ce “A yanzu muna sayar da kowane kwano na gawayi naira dari biyu, muna sayar da buhun gawayi naira dubu uku zuwa dubu biyu da dari takwas.”

Tashin farashin gas da kalansir

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masana sun yi gargadin cewa tsadar gas da kalanzir za ta kara janyo matsalar sare itatuwa.

Sai dai masana muhalli sun yi gargadin cewa muddin ba a dauki matakin shawo kan tashin farashin gas da kalanzir din ba,  jama'a za su ci gaba da sare bishiyoyi, abin da zai haifar da gurbatar muhalli da kuma yunwa.

Dr Salihu Umar Anka, babban jami'i ne a daya daga cikin kungiyoyi masu rajin kare muhalli, ya ce suna cikin fargaba.

 "Fargabarmu ita ce ana tufka da warwara kenan, bayan ana ware kudi ana yi wa manyan kasashe alkawura cewa ga abin da ake ciki cewar mun dauki alkawuran za mu rage wadannan matsaloli, to sai ga shi talaka da kuma masu kudin na komawa amfani da itace.

Masanin ya ce wannan babbar barazana ce ga tsirran da ake da su.

Tsirran da ake da su na gargajiya suna taimakawa wajan dore kasan noma domin a samu inganttaccen abinci.

Ba za ka iya dakile sare bishiyoyi ba, idan baka samar da makamashi mafi sauki da mutum zai yi amfani da shi ba.