Man Utd na farautar Dani Olmo, Lukaku na dab da tafiya Saudiyya

Dani Olmo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta shiga sahun masu farautar ɗan wasan Sifaniya Dani Olmo, wanda yarjejeniyarsa a RB Leipzig ke iya ba shi damar tafiya wata ƙungiyar kan fam miliyan 52. Ɗan wasan gefen mai shekara 25 ya ja hankalin ƙungiyoyi irinsu, Real Madrid da Manchester City da Chelsea da Tottenham. (Daily Mail)

Wakilan Manchester United sun je Sifaniya domin farautar 'yan wasa, kuma ɗan wasa Joselu mai shekara 25 da ke zaman aro a Real Madrid daga Espanyol, na cikin wadanda suke son sayewa. (Relevo - in Spanish)

United za kuma ta biya akalla yuro miliyan 60 kan ɗan wasan Brazil mai shekara 27, Gleison Bremer, da ke taka leda a Juventus, kuma watakil yarjejeniyar ta kunshi har da miƙa ɗan wasansu, Mason Greenwood, mai shekara 22. (Gazetta dello Sport - in Italian)

Manchester City da Newcastle United za su kalubalanci Manchester United kan saye ɗan wasan Everton da Ingila Jarrad Brathwaite, mai shekara 21. (Football Transfers)

Kungiyar Genoa ta Italiya na fatan karban tayi kan ɗan wasanta na gaba mai shekara 26 daga Iceland, Albert Gudmundsson, da ake alakantawa da Tottenham da kuma West Ham. (Fabrizio Romano)

Newcastle United ta kwaɗaitu da 'yan wasan Brazil da dama bayan wasan sada zumuncin da suka yi da Ingila a makon da ya gabata, ɗan wasan Barcelona Raphinha, mai shekara 27, da wanda ke tsare bayan Juventus Gleison Bremer, mai shekara 27, na cikin wadanda suke kauna. (Newcastle Chronicle)

Manchester United da Tottenham na farautar ɗan wasan Faransa, Jean-Clair Todibo, mai shekara 24, wanda ake kiyasata sayar da shi kan fam miliyan daga Nice a wannan kaka. (Talksport)

Crystal Palace na son saye ɗan wasan Valencia mai shekara 19, Cristhian Mosquera a wannan kaka amma tana fuskantar kalubale daga Atletico Madrid. (Evening Standard)

Chelsea za ta maye gurbin Todd Boehly a matsayin shugaba a 2027. (Mail)

Akwai kwarin gwiwar ɗan wasan Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 30, da ke zaman aro a Roma daga Chelsea, zai koma Saudiyya.(Calcio Mercato - in Italian)