Nketiah ya ci kwallo uku rigis a karon farko a Premier

An wallafa

Arsenal ta doke Sheffield United da ci 5-0 a wasan mako na 10 a gasar Premier League da suka kara a Emirates ranar Asabar.

Eddie Nketiah ne ya fara cin kwallo a minti na 28, bayan da aka koma zagaye na biyu ya kara na biyu, sannan ya ci na uku minti takwas tsakani.

Karon farko da ya zura uku rigis a raga a Premier League, kuma ɗan Ingila na biyu da ya yi wannan bajintar a Arsenal bayan Theo Walcott a wasa da West Brom a Mayun 2015.

Kawo yanzu Nketiah yana da kwallo biyar a raga idan aka haɗa da ukun da ya zura a ragar Sheffield da ɗaya da ya ci Fulham da Nottingham Forest.

Gunners ta zura kwallo na huɗu a ragar Sheffield ta hannun Fabio Vieira a bugun fenariti, sannan Takehiro Tomiyasu ya ci na biyar.

Wasa na 19 da Arsenal ke doke Sheffield a dukkan karawa tun bayan 1971, kuma Gunners ta yi nasara a wasa bakwai daga 10 da ta yi a bana.

Haka kuma karo na 37 da aka kasa doke Gunners a gida a wasa da sabuwar kungiyar da ta hau Premier tun bayan rashin nasara a hannun Newcastle a Nuwambar 2010.