Klopp ya taya Rashford murna da ya koma kan ganiya

Marcus Rashford

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya ce ''yana murna'' da dan wasan Manchester United, Marcus Rashford ya koma kan ganiya a tamaula.

Mai shekara 25 ya ci kwallo 25 a United a kakar nan, bayan da ya zura biyar a kakar 2021/22.

Liverpool za ta karbi bakuncin United a wasan mako na 26 a gasar Premier League ranar Lahadi a Anfield.

A wasan farko da suka buga a bana a Old Trafford, United ce ta ci 2-1, kuma tana ta ukun teburi, Liverpool tana ta shida.

''Abu ne mai wuya ka nuna murna kan wani abun ci gaba a Manchester United, idan kana kociyan Liverpool,'' in ji Klopp

''Amma ina taya Rashford murna da ya koma kan ganiya, domin ya fuskanci kalubale a bara, amma ya mance da komai ya mayar da hankali kan tamaula.''

Klopp ya kira United, wadda take ta uku a kan teburi, wadda ta lashe Carabao Cup a makon jiya da suna ''injin da ke samar da nasara''.

Rashford ne ya ci wa United kwallo na biyu da ta doke Newcastle United a Wembley ta lashe kofin farko tun bayan 2017.

United za ta buga FA Cup zagayen Quarter finals da Fulham cikin watan nan, za kuma ta fafata da Real Betis zagayen 'yan 16 a Europa League.