Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Arsenal za ta kai kwata fainal a Europa League?
Arsenal za ta karbi bakuncin Sporting Lisbon a wasa na biyu a Europa League ranar Alhamis a Emirates.
Kungiyoyin biyu sun tashi 2-2 a wasan farko zangon 'yan 16 da suka kara a Portugal ranar 9 ga watan Maris.
Dan wasan Arsenal, Eddie Nketiah na jinya, wanda ya ji rauni a farkon watan nan in ji Mikel Arteta.
Mai shekara 23 ya ci kwallo shida a wasa 12 a Gunners daga baya ya ji rauni.
Sai dai Gebriel Jesus da ya warke zai karawa Gunners kwarin gwiwa a wasa na biyu a Europa da za ta fuskanci Sporting ranar Alhamis.
Dan kwallon Brazil ya yi zaman benci ranar Lahadi a karawar da Arsenal ta ci Fulham 3-0 a Premier League, wanda ya shiga wasan a minti na 77.
Tsohon dan wasan Manchester City ya ji rauni a tawagar Brazil a lokacin gasar kofin duniya a Qatar a 2022, wanda Argentina ta lashe kofin.
Kenan za a fara wasa da shi a Arsenal a karon farko a fafatawa da Sporting tun bayan cikin Nuwamba.
Arteta ya ce Europa League ba za ta dauke hankalin Arsenal ba a kokarin da take na lashe kofin Premier League a karon farko tun bayan kusan shekara 20.
Rabon da Gunners ta dauki babban kofin gasar Ingila tun a kakar 2004 karkashin Arsene Wenger.
Arsenal tana mataki na daya a teburin Premier League da tazarar maki biyar tsakaninta da Manchester City ta biyu.
Arsenal ba ta taba lashe Europa League da Champions League ba.