Arsenal ta ci Tottenham gida da waje a kakar bana

An wallafa

Arsenal ta ci gaba da sa kaimi domin ta lashe Premier League na bana, bayan da ta doke Tottenham da ci 2-0 a ranar Lahadi.

Minti 14 da fara wasa Arsenal ta ci kwallo, bayan da Hugo Lloris ya ci gida, kuma karon farko da ya ci gida a wasa 354 da ya tsare raga a Premier League.

Minti na 36 kyaftin din Arsenal Martin Odegaard ya kara na biyu, wanda ya zura na takwas a bana kuma na 18 jumulla da yake da hannu aka zura a raga.

Da wannan sakamakon Arsenal ta bai wa Manchester City tazarar maki takwas a teburin Premier League.

A cikin watan Oktoba Arsenal ta ci Tottenham 3-1 a gasar Premier League a Emirates.

Rabon da Arsenal ta ci Tottenham gida da waje a Premier League tun a kakar 2013/14, inda Gunners ta ci 1-0 a Satumbar 2013.

A wasa na biyu kuwa a gidan Tottenham, Arsenal ta yi nasara da ci 1-0 a watan Maris din 2014.

Arsenal ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier League da maki 47, sai City ta biyu mai maki 39, sannan Newcastle da Manchester United masu 38 kowacce.

Ranar Lahadi 22 ga watan Janairu, Arsenal za ta karbi bakuncin Manchester United a Emirates a wasan Premier League.