Yadda ake zaƙulo gawarwaki a kowanne saƙo a Gaza

    • Marubuci, Joel Gunter
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporting from Jerusalem
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

A ranar Litinin, wadda ta kasance ranar farko ta zaman lafiya a Gaza, masu aikin ceto da fararen hula sun fara gano girman ɓarnar da aka yi a yankin.

Hukumar tsaron farar hula ta Gaza - wadda ita ce babbar hukumar bayar da agajin gaggawa ta yankin - ta ce tana fargabar akwai gawarwaki fiye da 10,000 waɗanda har yanzu ke binne a ƙarƙashin baraguzan gine-gine.

Kakakin hukumar Mahmoud Basal ya shaida wa BBC cewa, suna fatan za su iya kammala zaƙulo gawarwakin waɗanda suka mutu cikin kwana 100, amma akwai yiwuwar samun jinkiri sakamakon rashin wasu muhimman kayan aiki.

Sabbin hotuna daga Gaza bayan tsagaita wutar da aka yi a ranar Lahadin da ta gabata sun nuna irin barnar da aka yi a tsawon watanni 15 da Isra'ila ta kwashe tana luguden wuta , musamman a arewacin yankin.

A baya dai, Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa an lalata ko kuma ruguza kimanin kashi 60 cikin 100 na gine-ginen da ke Gaza.

Duk da cewa a yanzu murnar da jama'a ke yi ta maye ƙarar bama-bamai, a lokacin da tasagaita wutar ta fara aiki a ranar Lahadi, mutane sun ci gaba da kasancewa cikin mawuyacin hali a sassan Gaza.

A cewar hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP, yaƙin ya raba mutanen Gaza sama da miliyan biyu da matsugunansu, ga matsalar rashin samun kuɗin shiga, inda suka dogara kacokan kan agajin abinci domin ci gaba da rayuwa.

Wannan agajin ya fara shiga Gaza ne nan take bayan tsagaita wuta a ranar Lahadin da ta gabata kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce aƙalla manyan motocin dakon kaya 630 ne suka shiga cikin yankin a wannan ranar.

A ranar litinin kuma, wasu manyan motocin ɗaukar kaya 915 sun shiga yankin, in ji Majalisar, adadi mafi yawa tun farkon yaƙin watanni 15 da suka gabata.

Sam Rose, muƙaddashin daraktan, hukumar kula da Falasɗinawa ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) a Gaza, ya ce samar da kayayyakin agajin shi ne matakin farko cikin ƙalubalen da ke tattare da farfaɗo da rayuwa a zirin.

"Ba wai muna magana ne game da abinci da kiwon lafiya da gine-gine da tituna da sauran kayayyakin more rayuwa ba ne kaɗai, muna da ɗaiɗaikun mutane da iyalai da al'ummomin da ke buƙatar sake farfaɗo da su," in ji shi.

"Mawuyacin halin da suka fuskanta da wahala da rashi da baƙin ciki da wulakanci, da zaluncin da suka sha a cikin watanni 16 nan da suka gabata - farfaɗowarsu za ta ɗauki lokaci mai matuƙar tsayi."

A Isra'ila, iyalan mutane ukun da aka yi garkuwa da su da aka fara sakowa a musayar farko sun yi magana a wani taron manema labarai a Tel Aviv a daren ranar Litinin.

Mandy Damari, mahaifiyar Emily Damari, ta ce Emily tana cikin "ƙoshin lafiya" kuma "ta kama hanyar murmurewa" duk da cewa ta rasa yatsu biyu a harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoba 2023.

Meirav Leshem Gonen, mahaifiyar Romi Gonen, ta ce: "Romin mu ta dawo gida, amma duk iyalai sun cancanci samun sakamako iri ɗaya, da masu rai da matattu. Muna taya sauran iyalai jimamin wannan lamari."

Kafin taron manema labaran, hukumomin Isra'ila sun fitar da sabbin bidiyo da ke nuna Damari mai shekaru 28 da Gonen mai shekaru 24 da Doron Steinbrecher, mai shekaru 31 yayin da suke rungumar iyayensu mata a ranar Lahadi, ƴan sa'o'i kaɗan kafin a fitar da su daga Gaza.

Idan mataki na farkon tsagaita wutar ya ci gaba kamar yadda aka tsara, za a sake sakin wasu mutane 30 da aka yi garkuwa da su daga Gaza nan da kwanaki 40 masu zuwa, inda za a yi musayarsu da Falasɗinawa kusan 1,800 da za a sako daga gidajen yarin Isra'ila.

Hukumomin lafiya na Falasɗinu sun ƙiyasta cewa sama da mutane 46,900 ne aka kashe a Gaza a cikin tsawon sama da watanni 15 da aka shafe ana gwabza yaƙi yayin da wasu fiye da 110,700 da suka samu raunuka.

Ma'aikatar ba ta bambance tsakanin fararen hula da mayaƙa ba amma ta ce akasarin waɗanda suka mutu mata ne da ƙananan yara - iƙirarin da Majalisar Dinkin Duniya ta gaskanta.

Wani bincike da Birtaniya ta jagoranta wanda mujallar kiwon lafiya The Lancet ta wallafa a wannan watan ya nuna cewa akwai yiwuwar alƙaluman ma'aikatar kiwon lafiya sun gaza zahirin adadin waɗanda suka mutu da fiye da kashi 40 cikin 100.

Hukumar tsaron farar hula ta Gaza ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa, an kashe ko jikkata kashi 48% na ma'aikatanta a lokacin rikicin, yayin da aka lalata kashi 85% na motocinta, an kuma ruguza 17 cikin 21 na ofisoshinta.

Duk da cewa babu fargabar luguden wuta daga sama a halin yanzu, aikin sauran ma'aikatan hukumar na ci gaba da gudana. Hotunan da ma'aikatan suka aika wa BBC daga arewacin Gaza ranar Litinin sun nuna irin aikin da suke gudanrwa, wanda ya haɗa da zaƙulo gawarwakin jarirai da sauran mutanen da suka mutu.

Duk hanyar da ka bi za ka ci karo da gawarwaki. A kowace unguwa akwai gawarwaki a maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da suka ruguje,'' In ji Abdullah Al-Majdalawi, wani ma'aikacin hukumar mai shekara 24 da ke aiki a Birnin Gaza.

''Ko bayan tsagaita wutar mun samu kira daga mutane da dama suna cewa, ku zo don Allah iyalai na sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai.''

Malaak Kasab, wata mai shekaru 23 da ta kammala karatun digiri a baya-bayan nan wadda kuma ta yi gudun hijira daga birnin Gaza, ta shaida wa BBC a ranar Litinin cewa ƴan'uwanta na cikin waɗanda har yanzu ba a gano inda suke ba.

"Mun yi asarar ƴan'uwa da dama kuma wasu na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da suka ruguje," in ji ta. "Akwai mutane da yawa a ƙarƙashin ɓaraguzan - kowa ya san da wannan."

Gidan dangin su Kasab da ke cikin wani bene bai ruguje gaba ɗaya ba, in ji ta, amma ya lalace sosai. "Babu ƙofofi, babu tagogi, babu ruwa, babu wutar lantarki, babu komai, ko itacen da za a kunna wuta babu, ba za a iya rayuwa a ciki ba."

Har yanzu zirga-zirga na cike da haɗari ga mutanen Gaza da suka rasa matsugunansu yayin da sojojin Isra'ila ke shiri janyewa daga yankunan da ke da yawan jama'a a Zirin.

Rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta gargaɗi jama'a da kada su kusanci jami'anta ko cibiyoyinta, kuma kada su shiga wuraren da ta jibge dakaru a kusa da kan iyakar Gaza da kuma kusa da mashigar Netzarim, wanda ya raba yankunan arewaci da kudancin Gaza.

Amma akasarin mazauna yankin sun ƙagara su ga abin da ya rage na gidajensu kafin lokacin da aka ba su damar yin hakan. Hatem Eliwah, wani mai shekara 42 da ke aikin kula da masana'anta a birnin Gaza, ya ce yana tunanin tashi da kafa daga matsuguninsa da ke Khan Younis a kudancin ƙasar.

"Mun daɗe muna jiran wannan tsagaita wuta kamar yadda mutane ke jiran shiga aljannah," in ji Eliwah. "Na rasa ƴan'uwana guda biyu da iyalansu. Na rasa ƴan'uwana da kawuna, abin da nake fata yanzu kawai shi ne in koma gida."

Akwai matuƙar damuwa daga ɓangarorin biyu cewa yarjejeniyar na iya rugujewa tun kafin a kammala mataki na farko cikin kimanin makonni shida, kuma Isra'ila ta nanata cewa ta na da haƙƙin ci gaba da ɗaukar matakan soji a Gaza a kowane lokaci.

Da yake magana a taron kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin, Sakatare-Janar Antonio Guterres ya yi maraba da yarjejeniyar a matsayin "kyakkyawar fatan ci gaba" kuma ya ce dole ne a cika duka sharuɗɗan da aka gindaya a cikinta.

Sai dai Guterres ya yi gargaɗi game da taɓarɓarewar al'amura a yankin Gaɓar yamma da kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, wanda ya ga ƙaruwar hare-haren ƴan Isra'ila kan ƙauyukan Falasdinawa tun bayan harin da Hamas ta kai Isra'ila a ranar 7 ga Oktoban 2023.

"Manyan jami'an Isra'ila sun fito fili suna magana game da mamaye ɗaukaci ko kuma wani ɓangare na Gaɓar a cikin watanni masu zuwa," in ji Guterres, ya ƙara da cewa: "Duk irin wannan mamaya za ta zama babban cin zarafin dokokin ƙasa da ƙasa."