Falasɗinawa na fargabar rayuwa ba tare da agajin Unrwa ba saboda haramcin Isra'ila

    • Marubuci, Ziad Ghandour
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
    • Marubuci, Fernando Duarte
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Haramcin da Isra'ila ta ɗora wa hukumar agagaza wa Falasɗinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya (Unrwa) zai fara aiki nan gaba a cikin watan nan, inda zai hana ta gudanar da aikin agaji a Gaza da kuma wuraren da Isra'ilar ta mamaye.

Ƙungiyoyi da ƙasashen duniya sun nuna damuwa sosai game da matakin, suna cewa zai yi tasiri sosai kan Falasɗinawa musamman a Gaza.

Me hana Unrwa aiki ke nufi ga Falasɗinawa kuma me ya sa Isra'ila ta daɗe tana sukar hukumar?

Sama da shekara ɗaya kenan da ɓarkewar yaƙi a Gaza, ba yaƙin ne kawai ya fi damun wata mahaifiyar yara biyu ba mai suna Jumana Emad, har da gwagwarmayar neman abinci da ruwan sha mai tsafta.

Jumana mai shekara 26, 'yarjarida ce da ke zaune a Khan Younis da ke kudancin Gaza, kuma ta ce yanayin ya ta'azzara sosai a yanzu fiye da kodayaushe tun bayan fara yaƙin.

"Babu abinci ko abin sha. Ina da jaririyar da ke buƙatar abubuwa da yawa, amma babu komai."

Kamar sauran mazauna Gaza, Jumana ta dogara ne kan kayan tallafi da Unrwa ke bayarwa, inda kusan kowa ya dogara da ita tun kafin da kuma bayan aukuwar yaƙin.

Hukumar da aka kafa a shekara 1949, Unrwa ta fara kula da Falasɗinawa 750,000 da aka tilasta wa barin gidajensu bayan ƙirƙirar yankin Isra'ila. Ta zama hukumar agaji mafi girma a Gaza mai ma'aikata 13,000, da kuma fiye da 30,000 a faɗin Gabas ta Tsakiya.

Yanzu tana kula da kusan Falasɗinawa miliyan 5.9 da suka yi rajista a fadin yankin, ciki har da Jordan, da Lebanon, da Syria.

Ban da agajin abinci da sauran kayayyaki, tana gudanar da ayyukan da ya kamata a ce na gwamnati ne, kamar makarantu, da kiwon lafiya, da gina tituna, har ma da bai wa 'yankasuwar Falasɗinawa bashi.

Amma ta yi gargaɗin cewa aikinta Gaza da Gaɓar Yamma zai iya zuwa ƙarshe nan gaba kaɗan idan haramcin ya fara aiki ranar 28 ga watan Janairu.

'Yanmajalisardokokin Isra'ila 92 ne suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da haramcin, yayin da 10 ne kacal suka nuna adawa. Gwamnatin Isra'ila ta sha zargin hukumar da haɗa kai da ƙungiyar Hamas wajen kai harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Unrwa ta ce duk wata hulɗa da ta yi da Hamas ta yi ne kawai domin samun damar gudanar da ayyukanta. Ta ce Isra'ila ba ta taɓa bayyana hujja ba kan zarge-zargen da take yi mata.

Hamas ce ka emulkin Gaza tun lokacin da ta ƙwace mulki daga jam'iyyar Fatah a 2007.

Yayin da sabuwar dokar za ta haramta ayyuka a Gabashin Ƙudus da kuma Isra'ila, za kuma ta hana ma'aikatan hukumar hulɗa da jami'an Isra'ila.

A aikace, Unrwa ta ce hakan zai sa ta kasa yin komai a Gaza da Gaɓar Yamma saboda ta dogara ne kan yarjejeniyarta da Isra'ila wajen gudanar da ayyuka, ciki har da hanyoyin da take bi wajen kai kayan agaji a faɗin yankin.

Kamar ita ma ƙungiyar Palestinian Red Crescent, Unrwa na aiwatar da ayyukan agaji ne a cibiyoyi 11 na Gaza.

Tun bayan fara yaƙin, Unrwa ta ce ta raba ƙunshin kayan abinci ga mutum miliyan 1.9.

"Idan aka aiwatara da haramcin, hakan na nufin ayyukan Unrwa a Gaɓar Yamma - ciki har da Gabashin Ƙudus - da Gaza zai iya zuwa ƙarshe," a cewar Roland Friedrich, shugaban sashen ayyuka na Unrwa a Gaɓar Yamma.

"Gaɓaer Yamma kaɗai, kenan yaran Falasɗinawa 47,000ba za su je makaranta ba. Sannan sama da rabin miliyan da ke samun tallafin kiwon lafiya ba za su samu ba."

Ilimi na fuskantar barazana

Unrwa ta fara bai wa Falasɗinawa ilimi tun shekarun 1950, lokacin da hukumar ta fara kafa makarantunta.

Yanzu tana kula da ɗaruruwan makarantu a Gaza, da Gaɓar Yamma, da Jordan, da Lebanon, da Syria.

Hakan na nufin makarantunta da ke cikin Zirin Gaza na fuskantar barazanar rufewa.

A lokacin yaƙin, akasarin makarantun Gaza sun koma mafaka ga Falsɗinawan da hare-haren Isra'ila suka raba da muhallansu. Unrwa ta ce kashi 70 cikin 100 na makarantun an kai musu hari - inda aka ruguza wasu ko aka lalata su sosai.

Unrwa ta ce kashi 95 cikin 100 na makarantun da aka kai wa harin, ana amfani da su ne a matsayin wurin fakewar 'yan gudun hijira.

"Lokacin da muka fara jin maganar haramcin, nan take iyaye suka fara tambayar mu game da tasirin hakan a kan 'ya'yansu," a cewar Doaa Al-Zorba, wata malama a makarantar Unrwa ta Shu'fat da ke Gabashin Ƙudus tsawon shekara 20.

"Kawai muna ce musu lamarin ya fi ƙarfinmu."

Shekaru ana cecekuce

Haramta ayyukan Unrwa na zuwa ne bayan zarge-zargen da Isra'ila ta sha yi kan ma'aikatan hukumar na alƙarsu da Hamas wajen kai harin ranar 7 ga watan Oktoba.

A watan Janairun 2024, Isra'ila ta yi iƙirarin cewa ma'aikatan Unrwa 12 ne suka shiga cikin mayaƙan Hamas da suka kai hari a kudancin Isra'ila da ya kashe mutum 1,200 da kuma sace wasu.

Ƙasashe da dama kamar Amurka, da Birtaniya, da Jamus sun dakatar da bayar da kuɗaɗen gudanar da Unrwa saboda iƙirarin, amma daga baya sun sauya shawara.

Wani bincike da MDD ta gudanar kan ma'aikatan Unrwa 19 ya gano cewa akwai yiwuwar tara daga cikinsu sun shiga hare-haren - an kori waɗanda ke da rai a lokacin daga aikin.

Daga baya Isra'ila ta yi iƙirarin cewa ma'aikatan Unrwa sama da 450 mambobin ƙungiyoyin 'yan bindiga ne, amma binciken MDD a watan Agusta ya ce Isra'ila ba ta bayar da wata hujja ba game da hakan.

Gwamnatin Isra'ila ta kuma bayyana adawa da ayyukan koyarwa na hukumar, musamman litattafan da take amfani da su - waɗanda Isra'ila ta ce suna koya wa yara ƙiyayyarta.

A 2022, wata hukumar Isra'ila mai suna IMPAC-see ta ce kayayyakin karatu na Unrwa na nuna cewa Isra'ila na ƙoƙarin "shafe Falasɗinawa daga ban ƙasa".