Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
West Ham za ta aro Maguire, Garnacho ya ki yarda da albashin Utd
West Ham na shirin dauko aron dan bayan Ingila Harry Maguire,daga Manchester United. (Mirror)
Har yanzu Alejandro Garnacho bai yarda ya kulla sabuwar yarjejeniya da Manchester United ba, saboda wakilan dan kasar ta Argentine na son a kara wa dan gaban albashi a kan fam 20,000 da ake ba shi a mako.
Wannan ya sa Real Madrid da Juventus suke jiran tsammani a kan matashin dan wasan mai shekara 18 wanda kwantiraginsa zai kai har 2024, da kuma yuwuwar tsawaitawa da shekara daya. (Independent)
Arsenal ta tuntubi Bayer Leverkusen a kan dan gabanta Moussa Diaby amma kuma kungiyar ta Jamus ba ta son sayar da dan Faransar mai shekara 23 a watan Janairu. (Sky Sports)
Barcelona na matukar son daukar dan wasan tsakiya na Jamus Ilkay Gundogan a rahusa da bazara lokacin da kwantiraginsa zai kare da Manchester City . (Telegraph)
Chelsea na jiran tsammani a kan dan gaban Brighton Leandro Trossard, wanda ake dangantawa da tafiya Arsenal ko Tottenham, amma kuma ana ganin abu ne mai wuya kungiyar tasa ta karbi kudin da yake kasa da fam miliyan 25 a kan dan Belgium din. (Mirror)
Fiorentina ta yi watsi da tayin fam miliyan 30 da Leicester City ta gabatar mata a kan dan gabanta na Argentina Nicolas Gonzalez. (90 Min)
Southampton na dab da tabbatar da zaman dindindin na matashin dan gaban Senegal Nicolas Jackson, wanda Villarreal ta sa masa farashin yuro miliyan 20m. (Athletic)
Crystal Palace na son dawo da dan wasan tsakiya na Chelsea Conor Gallagher kungiyar saboda yadda matashin na tawagar Ingila ya taka rawar-gani a lokacin da yake zaman aro a Eagles din a kakar da ta wuce. (Sky Sports)
Darektan wasanni na Napoli Cristiano Giuntoli ya ce yana da kwarin guiwa kungiyar za ta iya sayen matashin dan wasan tsakiya na Angers da Morocco Azzedine Ounahi, wanda kuma ake dangantawa da tafiya Aston Villa da Leeds United.(Sport Mediaset)
Wakilin dan bayan Belgium Yannick Carrasco ya ce ana tattaunawa kan tafiyarsa Barcelona daga Atletico Madrid, yayin da shi kuwa dan gaban Holland Memphis Depay, zai bar Barcelona zuwa Atletico Madrid din. (Nieuwsblad)
Borussia Monchengladbach ta yi watsi da tayin da Bayern Munich ta gabatar mata na yuro miliyan 8 da karin yuro miliyan 1 a kan golan Switzerland Yann Sommer, mai shekara 34. (Florian Plettenberg)
Tsohon kociyan Leeds United Marcelo Bielsa shi ne hukumar kwallon kafa ta Mexico ke son nadawa a matsayin sabon kociyan tawagar kasar. (ESPN)
Ana sa ran golan Jamus Loris Karius, ya tsawaita kwantiraginsa a Newcastle United har zuwa bayan watan Janairu, yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu. (Mail)