Abinda ya kamata ku sani kan wasan Man United da Chelsea

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United za ta karbi bakuncin Chelsea a wasan mako na 15 a gasar Premier League ranar Laraba a Old Trafford.

United tana mataki na bakwai a teburin Premier League da maki 24, ita kuwa Chelsea mai maki 19 tana ta 10 teburin.

Wasan da suka buga a bara:

Premier League ranar 25 ga watan Mayun 2023

  • Manchester United 4 - 1 Chelsea

Premier League ranar 22 ga watan Oktoban 2022

  • Chelsea 1 - 1 Manchester United

Chelsea ta kasa cin Manchester United a wasa 11 baya tun bayan rashin nasara 1-0 a Stamford Bridge a Nuwambar 2017, wadda ta yi nasara hudu da canjaras bakwai.

Wasan karshe da Chelsea ta yi nasara a United shi ne 1-0 a watan Mayun 2013, kenan ta yi canjaras shida aka doke ta karo hudu a wasa 10 baya a Old Trafford.

An yi canjaras 26 a Premier League tsakanin Manchester United da Chelsea, shi ne wasan da aka fi canjaras a tarihin gasar.

Manchester United

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta yi rashin nasara uku a wasa biyar baya a Premier League.

United ta kasa cin kwallo kafin hutu a gida a karawa shida daga bakwai.

Idan aka doke United zai zama karo na 18 a dukkan fafatawa a 2023, karon farko da za ta yi rashin nasara da yawa a shekara tun bayan 1989.

United ta yi rashin nasara 17 a dukkan karawa a 2023, karon farko da aka doke ta wasa da yawa tun 2001, idan ya kai 18 shi ne mafi yawa a tarihi tun 1989.

Har yanzu United ba ta yi canjaras ba, tun bayan 2-2 da ta yi da Tottenham ranar 27 ga watan Afrilu, ta ci wasa 13 an doke ta takwas daga fafatawa 21.

Marcus Rashford ya ci kwallo biyu a wasa 18 a United a bana, bai zura kwallo ba a raga a wasa 10 baya a Old Trafford.

Chelsea

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta yi rashin nasara 16 daga 37 a 2023, a 1993 aka doke ta wasa 20 a Premier League a shekara daya.

Kungiyar Stamford Bridge ta ci wasa uku daga hudun da ta yi a waje, fiye da nasarar da ta samu a fafatawa 16, wadda ta yi canjaras biyar da rashin nasara tara.

Ta yi nasara a wasa daya daga 10 da ta kara a tsakiyar mako a Premier League da canjaras uku da rashin nasara shida, wadda aka doke karo biyar daga shida ranar Talata ko Laraba ko kuma Alhamis.

Kowanne wasan Chelsea uku a waje da ta buga a bayan nan an tashi 4-1 da cin karawa biyu da rashin nasara daya.

Ranar 25 ga watan Mayu, United ta doke Chelsea 4-1 a Old Trafford.

Kungiyar da Mauricio Pochettino ke jan ragama ta yi wasa bakwai ana zura mata kwallo, wadda jimilla 16 suka shiga ragarta.

Kungiyar Manchester United ita ce wadda Raheem Sterling ya fuskanta da yawa sau 24 a lik da kofi, amma bai zura mata kwallo a raga ba.