Man United ta caskara West Ham a Premier ranar Lahadi

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta caskara West Ham 3-0 a wasan mako na 23 a Premier League ranar Lahadi a Old Trafford.
United ta fara cin kwallo a minti na 23 da take leda ta hannun Rasmus Hojlund, kuma haka suka je hutu kungiyar Old Trafford na cin 1-0.
Bayan da suka yi hutu ne suka koma karawar zagaye na biyu United ta kara na biyu ta hannun Alejandro Garnacho, sannan ya kara na uku saura minti shida a tashi na biyu da ya ci a wasan.
Wannan shi ne karo na uku da United ta ci wasa uku a jere, tun bayan watan Oktoba, kuma karo na biyu da ta yi wannan bajintar a kakar bana.
Ranar 28 ga watan Janairun 2024, United ta fitar da Neewports Co da ci 4-2 a FA Cup a zagaye na hudu.
Wasa na biyu a jere da kungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama ta ci shi ne ranar 1 ga watan a Premier League ta je ta yi nasara a kan Wolves ta cin 4-3.
Mai tsaron ragar Manchester United, Andre Onana ya taka rawar gani, wanda ya hana kwallon Ben Johnson da na Mohammed Kudus shiga raga.
A wasan farko da suka fuskanci juna a Premier League a bana, West Ham ce ta yi nasara 2-0 ranar Asabar 23 ga watan Disambar 2023.
Da wannan sakamakon United tana mataki na shida a kan teburi da maki 38, bayan wasa 23 da tazarar maki biyu tsakaninta da West Ham wadda take ta bakwai.
United za ta kara a wasan mako na 24 a Premier League ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairu, wadda za ta ziyarci Aston Villa a Villa Park.
A kuma ranar ce West Ham za ta karbi bakunci a wasan hamayya tsakanin kungiyoyin Landan a babbar gasar tamaula ta Ingila.












