Yadda yarinyar da ke son zama ƴar sama-jannati ta nutse a gaɓar tekun Italiya

Asalin hoton, OTHER
Burin Maeda Hussaini shi ne na ganin ta zama ƴar sama jannati, inda haka ne ma ya sa ta rubuta wasika zuwa ga hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka.
Abu ne mai wahala ga Maeda ƴar shekara 17 da kuma ta kasance ‘yar Afghanistan.
Ko da lokacin da iyayenta suka tsere wa Afghanistan zuwa Iran bayan da Taliban ta ƙwace iko a watan Agustan 2021, Maeda ta ki saduda kan burin nata.
Babban burinta shi ne zuwa Turai domin ci gaba da karatunta.
Ta yanke shawarar yin tafiyar ƙasa zuwa Turkiyya ta hanyar tsallakawa teku. Mahaifiyarta ba ta amince da batun ba da farko, amma sai Maeda ta ƙarfafa mata gwiwar cewa babu abin da zai faru.
"Na faɗa mata cewa ki je ƴata, Allah ya kare ki,’’ in ji Mahtab Forough. “Na san za ta iya saboda ni na haifeta.”
Maeda ta kasance cikin mutum 200 da suka shiga jirgin ruwa zuwa Turkiyya a ranar 22 ga watan Febrairun. Kwanaki huɗu bayan nan, sai jirgin ya rabe a tekun Italiya kusa da garin Crotone.
"Ina gaisuwa Mama, ina fatan kina lafiya. Lafiya ta ƙalau ni ma. Har yanzu ina cikin jirgi. Za mu isa nan da minti 30.”
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Magana ta ƙarshe ke nan da Mahtab, mahaifiyar Maeda ta ji daga wajen ƴarta, inda daga nan ba abin da ta ji sai ƙarar jirgin da ke tafiya cikin ruwa.
Daga bisani sai ta samu saƙon karta-kwana.
"Mahaifiyata, gani nan na kusa shiga Italiya, yanzu za mu sauka, lafiya ta ƙalau. Kar ki saka wa kanki damuwa.”
Abu ne da ba a saba gani ba na mata matasa su yi tafiya su kaɗai saboda irin haɗura da ke tattare da tafiyar, amma Mahtab ta ce babbar ƴarta na cike da burin ganin mafarkinta ya zama gaske.
Watanni bakwai kafin nan, an harbi Maeda a ƙafa a lokacin da ta ke tsallake iyaka daga Iran zuwa Turkiyya.
Sai dai, hakan bai sa ta ji wani abu ba na tsawon kwanaki goma ko kuma karya mata gwiwa.
Iyalanta sun ce ta shiga haɗura daban-daban a ƙoƙari da ta ke na tsallakawa zuwa Turai.
"Na shiga damuwa a kanta, inda na ce mata da ta dawo gida,’’ in ji mahaifiyarta. “Na faɗa mata, baki gaji da yunƙurin zuwa Turai da kike ta yi ba?”
Aƙalla mutum 70 ne suka mutu ta wannan hanyar. Sai dai, har yanzu ba a kai ga gano gawar Maeda ba.
Tafiya mai cike da haɗari
Turkiyya ta zama wurin da ƴan Afghanistan ke zuwa kafin tsallakawa zuwa Turai. Wasu na bi ta tsibirin Balkans ko kuma tsallakawa ta ruwa domin isa ƙasashe irin Italiya.
A 2022, ƴan Afghanistan da aka bai wa mafaka sun kai kashi 13 a cikin mambobin ƙasashe na Tarayyar Turai da Switzerland da kuma Norway, a cewar alƙaluman hukumomi.
Wani ɗan Iran ya yanke shawarar fasa irin wannan tafiyar daɓ da lokacin da zai tashi.
"An faɗa mana cewa jirgin zai ɗauki mutum 60 zuwa 70,’’ in ji Saman, wanda ba shi ne sunansa na asali ba.
"Amma a daren mun yi niyyar barin Santanbul zuwa Izmir a cikin wata babbar mota, daga baya mun gano cewa mun kai 117, yawanci ƴan Afghanistan.”
"Kamar mummunan mafarki ne. Har yanzu ban yarda da abin ba,’’ inda yake tuna yadda Allah Ya kare shi afkawa cikin haɗura da ke kan hanyar. “Ban sake yarda da wani abu ba a yanzu. Rayuwa ba komai ba ce.”
Wasu mutum biyu da suka tsira, sun faɗa wa BBC cewa jirgin ya rabe gida biyu jim kaɗan bayan barin tekun Turkiyya.
Sun ce nan da nan, masu tsallakar da mutane ta hanyar suka kawo wani jirgi, inda aka mayar da mutane zuwa cikinsa.
Wani ɗan Afghanistan da ya tsira wanda muke kira da Meraj, ya ce tafiyar na cike da haɗari, amma sun ji sauki lokacin da suka kusa sauka.
"Wani jirgi ya nufo mu tare da kunna fitilunsa a kan jirginmu. Waɗanda ke kula da jirginmu sai suka shiga fargaba, inda suka yi kokarin juya jirgin zuwa wani wuri,’’ in ji Meraj.
"Jirginmu ya juya sau ɗaya, sai ya sake juyawa, ya kuma ƙara juyawa a karo na uku, inda ya bugi wani abu mai ƙarfi tare da rabewa gida biyu. Iyalai da yara na ƙasa yayin da maza da kuma wasu ƴan gudun hijira na saman jirgin,’’in ji Meraj.
"Na tuna lokacin da ruwa ya fara shiga cikin jirgin, ya zo har kan wuyana, inda a nan na ji ɗanɗanon mai, sai kawai na suma. Ban sake sanin me ya faru ba.”
Meraj na cikin mutum ɗaya da ruwa ya yashe zuwa bakin gaɓa cikin mutane 80. Ba a dai makomar sauran ƴan uwansa da ke cikin jirgin ba.
Hukumomin Italiya sun kama mutum uku, da suka haɗa da ɗan Turkiyya ɗaya da kuma ‘yan Pakistan biyu, waɗanda ake kyautata zaton sun jagoranci tuƙa jirgin.
Ƴan sanda a Italiya sun ƙiyasta cewa kowane mutum ya biya $8,500 domin shiga jirgin.
A cewar ƙungiyoyin sa ido, sama da mutum 20, 000 ne suka mutu ko kuma suka ɓace a tsakiyar tekun Mediterranean tun 2014.
'Takalman ƴan uwana kaɗai na iya ganowa'
A lokacin da labarin hatsarin jirgin ya fara watsuwa, nan da nan iyalai suka fara isowa zuwa kudancin Italiya, da nufin gano ƴan uwansu da suka ɓata.
Laila Timory mai shekara 47, ta taho daga Jamus.
"Na ɗauka cewa zan sake ganin ɗan uwana bayan tsawon shekaru. Na ɗauki shekara bakwai ina jira domin na gan shi.”
Laila ta bar lardin Kunduz da ke Afghanistan a 2015. Har yanzu tana iya tuna irin rabuwa ta ƙanƙanin lokaci da ta yi da ɗan uwanta mai suna Zabih.
"Mun yafewa juna ko da bamu sake ganin juna ba.”
Zabih Timory mai shekara 33 da matarsa Mina mai shekara 23 da yaransu Haseeb da Arif da Akif dukkansu suna cikin kwale-kwalen.
Laila ta ce ɗan uwan nata lauya ne da ya yi aiki da gwamnatin Afgahnistan a baya, inda yaji tsoro bayan zuwan Taliban.
"Lokacin da na isa wajen da lamarin ya faru, abu na farko da na fara gani shi ne gawar yaron ɗan uwana Habeeb ɗan wata 18,’’ in ji Laila, yayin tattauna da BBC.
"Hukumomin Italiya sun ɗauke ni zuwa wani ɗaki, inda suka bani hotuna na duba ko zan iya gane wani a ciki.
Akwai hotunan waɗanda suka mutu da hotunan waɗanda ke kwance a asibiti da kuma na waɗanda suka tsira da ke cikin wani sansani. Sai dai ban ga hoton sauran ‘yan uwana ba.”
Daga nan Laila ta nufi bakin teku don duba ‘yan uwanta.
"Ba zan iya zama na jira ba, na ga takarcen jirgin, na kuma ga kayaki. Ina ji a jikina cewa ɗan uwana na binne a cikin ƙasa, inda suke jiran taimakona,’’ in ji Laila.
"Abin da na iya gano wa shi ne takalmansu kaɗai. Daga baya na sake gano rigar sanyi da kuma jakar matar shi.”
Laila da ƴarta basu sake gano wani abu ba bayan wannan. Fatan su shi ne na yadda za su ga gawarwakinsu ko da ruwa zai yashesu zuwa bakin gaɓa.
"Yana da matuƙar wahala. Mun samu labarin cewa rabin mutane da ke cikin jirgin sun nutse kuma suna ƙasan teku.
"Ba za a iya gane wasu gawarwakin ba, bayan zama cikin ruwa na lokaci mai tsawo,’’ in ji Laila.
"Abin da muke fata shi ne gano gawarwakin ‘yan uwan mu domin kai su zuwa gida a binnesu.”
Idan muka dawo Iran, iyayen Maeda na ci gaba da addu’ar samun labari mai daɗi. A matsayinsu na ƴan gudun hijira a Iran, sun kasa samun biza don yin tafiya zuwa Italiya domin nemo ƴarsu da kansu.
"Ina jiran ta," in ji mahaifiyar Mahtab. “ban bai wa kowa damar yi mata jana’iza ba. Ban kuma bawa wani ya yi min ta’aziyyarta ba.”
Tun bayan da Taliban ta ƙwace iko da mulki a Afghanistan, an tauye wa yaran mata da yawa ƴanci da suke da shi kamar na samun ilimi.
Tun da farko, Maeda ta yi fatan cewa da zarar ta isa Turai kafin ta cika shekara 18, za ta buƙaci iyayenta da wasu ƴan uwanta guda uku suma su je su sameta a can a cikin wani tsari na sake haɗa kan iyalai.
"Tana yawan cewa, 'Mahaifiyata don Allah kada ki aurar dani a cikin shekarun da nake ciki kamar ke.’’ In ji Mahtab.
"Ina da babban buri. Na san mahaifina mai ƙaramin ƙarfi ne, ba shi kuma da ƙarfin da zai iya kai ni karatu zuwa Turai.”











