Waiwaye: Ce-ce-ku-ce kan matatar Dangote da ƙoƙarin Tinubu na daƙile zanga-zanga
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Asalin hoton, ALIKO DANGOTE
A farkon wannan makon ne wani ce-ce-ku-ce ya ɓarke tsakanin hamshaƙin attajirin nan na nahiyar Afirka, Aliko Dangote da hukumomin gwamnatin Najeriya.
Matakin na zuwa ne bayan da Dangoten ya zargi wasu jami'an gwamnatin ƙasar da yi wa sabuwar matatar man da ya gina zagon-ƙasa.
Da fari kamfanin mai na ƙasar, NNPCL, ne ya yi zargin cewa sinadarin sulpur - da ke cikin man da ake tacewa a sabuwar matatar - ya zarta adadin da ake buƙata.
Ana haka kuma kwatsam! Sai Hukumar da ke sanya ido kan harkokin man fetur a Najeriya watau NMDPRA ta yi zargin cewa man ake tacewa a matata ba shi da inganci.
Lamarin da bai yi wa Dangoten daɗi ba, har ta kai shi ga bayyana cewa a shirye yake ya sayar wa NNPCL da matatar ta biliyoyin daloli.
Ƙoƙarin Tinubu na daƙile zanga-zanga

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
Tun bayan da wasu matasan Najeriya suka fara kiraye-kirayen gudanar da zanga-zanga ranar 1 ga watan Agusta, shugaban ƙasar Bola Tinubu ya fara tuntuɓar masu ruwa da tsaki a ƙasar da nufin dakatar da yunƙurin matasan.
Shugaban ƙasar ya gana da gwamnonin jihohin ƙasar da sarakunan gargajiya da malaman addinin Musulunci, duk dai a ƙoƙarinsa na dakatar da matasan.
Shugaba Tinubun kuma ya yi kira ga matasan ƙasar su jingine ƙudurin nasu, su kuma bai wa gwamnatinsa dama, yana mai cewa gwamnatin tasa na iya bakin ƙoƙarinta wajen magance matsalolin matsin tsadar rayuwa da ƙasr ke fuskanta.
Haka nan Tinubu ya umarci gwamnoni su koma jihohinsu domin ganawa da mutane tare da lallashin su kan batun zanga-zangar.
Manufar masu zanga-zanga ita ce "kifar da gwamnati" - DSS

Asalin hoton, DSS
A cikin makon ne di hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, DSS ta yi gargaɗi dangane da shirin zanga-zangar matsin rayuwa a ƙasar.
Hukumar ta DSS ta ce tuni ta riga ta gano waɗanda suka kitsa ta da masu goyon bayan zanga-zangar, inda suka gargaɗe su da su sanya kishin ƙasa su dakatar da shirin zanga-zangar.
Gargaɗin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Dakta Peter Afunanya ya aike wa manema labarai.
Sanarwar ta ce hukumar ta DSS ta gano cewa wasu ɓata-gari na shirin karkatar da akalar zanga-zanagr da manufar tayar da zaune tsaye a Najeriya.
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da ƙudirin sabon albashi mafi ƙanƙanta

Asalin hoton, Nigerian Senate/X
A makon ne kuma Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da ƙudurin sauya dokar albashi mafi ƙanƙanta bayan shugaban ƙasa ya aika da buƙatar.
Majalisar ta mince da kuɗirin ne da ke neman tabbatar da ƙarin albashi mafi ƙanƙanta daga N30,000 zuwa N70,000 bayan tsallake karatu na biyu da na uku ba tare da ɓata lokaci ba.
Matakin na zuwa ne bayan ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnatin tarayyar ƙasar sn amince da N70,000 bayan jerin tattaunawa tsakaninsu.
EFCC ta kama mutum huɗu da almundahanar kuɗi a Kano

Asalin hoton, EFCC/X
Haka kuma a makon ne jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Kano sun kama wani ma’aikacin banki tare da wasu ‘yan kasuwa guda uku da laifin almundahana ta kuɗi a jihar.
An kama mutanen ne a hanyar Unity Road, kasuwar Kantin Kwari a Kano, biyo bayan sahihan bayanan sirri dangane da mutanen da ake zargi da safarar wasu makudan kudade.
Bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun ƙware wajen karɓar kuɗaden Naira da suka lalace daga bankuna daban-daban, tare da cire wasu ‘yan kudade daga kowane bandir.
A lokacin da aka kama su, jami’an sun kwato naira miliyan 7.5 daga hannun waɗanda ake zargin.











