Bayern Munich ta fitar da Arsenal a Champions League

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Bayern Munich ta kai daf da karshe a Champions League, bayan da ta ci Arsenal 1-0 a Allianze Arena - kenan ta kai zagayen gaba da cin 3-2 gida da waje.

Joshua Kimmich ne ya ci kwallon a minti na 63, bayan da ya samu tamaula daga wajen Raphael Guerreiro.

A makon jiya ranar Talata kungiyoyin suka tashi 2-2 a wasan farko zagayen daf da na kusa da na karshe a Emirates.

Tun farko Arsenal ta yi fatan kai wa zagayen gaba, sakamakon da Bayern Munich ba ta kokari a kakar nan, wadda ta buga karawar ba Serge Gnabry da Kingsley Coman, wadanda ke jinya.

Arsenal wadda ta yi kokarin lashe Premier League da Champions League a kakar nan, yanzu an fitar da Gunners a gasar zakarun Turai.

Kenan kofin Premier League ke gabanta, wadda ta koma ta biyun teburi da maki 71 da tazarar maki biyu tsakaninta da Manchester City ta daya.

Arsenal wadda ba ta taba dauka Champions League ba ta kare kakar bara ba tare da daukar kofi ba.

Ranar Asabar Arsenal za ta je gidan Wolverhampton ranar Asabar a gasar Premier, kenan ba za ta yi sakacin kara barar da maki ba a sauran wasannin dake gabanta.

Haka Arsenal ta yi sakaci a bara da ta bari Manchester City ta karbe ragamar teburin Premier League, sannan ta lashe kofin, Gunners ta yi ta biyu.