Netzah Yehuda: Bataliyar Isra'ila da Amurka ke neman saka wa takunkumi kan yaƙin Gaza

Netzah Yehuda soldiers holding weapons

Asalin hoton, Nahal Haredi

    • Marubuci, By Alhareth Alhabashneh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
  • An wallafa

'Yansiyasar Isra'ila sun nuna ɓacin rai lokacin da suka ji labarin da ba a gama tabbatarwa ba cewa Amurka na yunƙurin saka wa bataliyar Netzah Yehuda ta ƙasar takunkumai.

Shafin jaridar intanet na Axios ya ce za a ɗauki matakin ne saboda cin zarafin ɗan'adam da dakarunta suka aikata a yankin Falasɗinawa na Gaɓar Yamma da Kogin Jordan - ko kuma West Bank a Turance.

Idan hakan gta faru, zai zama karo na farko kenan da wata gwamnatin Amurka ta saka wa wata bataliyar Isra'ila takunkumi.

Rundunar Sojin Isra'ila ta faɗa ranar Lahadi cewa "ba ta da masaniya game da wani takunkumin Amurka" kan bataliyar ta Netzah Yehuda, tana mai cewa filin yaƙi ne kuma ta yi aikinta bisa dokokin yaƙi na duniya.

Wani sojin bataliyar Netzah Yehuda kenan yake addu'a a Bangon Yamma na Birnin Ƙudus a 2007 a matsayin wani ɓangare na kammala horon soji

Asalin hoton, AFP / Getty Images

Bayanan hoto, Wani sojin bataliyar Netzah Yehuda kenan yake addu'a a Bangon Yamma na Birnin Ƙudus a 2007 a matsayin wani ɓangare na kammala horon soji

Idan Amurka ta saka wa bataliyar takunkumi, za a haramta wa Netzah Yehuda daga yin amfani da kowane irin kayan yaƙi na Amurka da kuma ba su horo, a cewar majiyoyi daga Amurka.

A 'yan watannin da suka gabata, an yi ta da jijiyoyin wuya kan yafe wa Yahudawan Haredi shiga aikin soji na hidimar ƙasa, saɓanin akasarin Isra'ilawa.

Aikin soji na hidimar ƙasa wajibi ne a Isra'ila, inda maza ke shafe shekara uku, mata kuma shekara biyu.

Kafar yaɗa labarai ta Isra'ila ta ruwaito cewa Amurka ta sha neman bayanai daga rundunar sojin Isra'ila game da wasu hare-haren da Netzah Yehuda suka kai kan Falasɗinawa.

Benjamin Netanyahu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce saka musu takunkuman 'zai zama ƙarshen rashin kyautawa'

'Ƙarshen rashin kyautawa'

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya nuna ɓacin ransa game da batun.

Ya siffanta lamarin a matsayin "ƙarshen rashin kyautawa da kuma lalacewar alaƙa".

Ministan Majalisar Yaƙi ta Isra'ila Benny Gantz ya ce saka wa sojojin Isra'ila takunkumi abu ne "mai haɗari". Ya nemi Amurka ta janye matakin lokacin da suka yi waya da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.

"Babu wata hujjar saka takunkumi saboda umarni ake ba su wanda kuma bai saɓa wa dokokin ƙasashen duniya ba," in ji shi.

Shi kuma Ministan Tsaro Itamar Ben-Gvir ya nemi a ƙwace kuɗaɗen da Amurka ke bai wa Hukumar Falasɗinawa saboda yunƙurin saka takunkuman.

An kafa bataliyar Netzah Yehuda ce da zimmar ɗiban matasan Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi aikin soji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kafa bataliyar Netzah Yehuda ce da zimmar ɗiban matasan Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi aikin soji

Ministan Kuɗi Bezalel Smotrich ya siffanta matakin a matsayin "shirme da kuma yunƙurin tilasta mana yarda da ƙasar Falasɗinawa".

Shi kuwa jagoran adawa Yair Lapid ya ce "rundunar sojin Isra'ila da shugabanninta ne ke fara jin tasirin kowane irin tasari a ɓangaren dokoki daga gwamnati", amma ya ce dole ne "a guji batun saka wa sojojin takunkumi".

A nasa ɓangaren, shugaban jam'iyyar Labor Party mai adawa, Merav Michaeli, ya nemi a rusa bataliyar ta Netzah Yehuda, yana mai cewa "an daɗe da sanin cinhanci da zalincinta tsawon shekaru".

Israeli soldiers of the Ultra-Orthodox battalion "Netzah Yehuda" take part in their annual unit training in the Israeli annexed Golan Heights

Asalin hoton, AFP / Getty Images

Bayanan hoto, Netzah Yehuda soldiers take part in training in 2014

Su wane ne dakarun bataliyar Netzah Yehuda?

Da yawa daga cikin Yahudawan Haredi ba su son shiga aikin soja saboda sukan sadaukar da rayuwarsu ne wajen nazarin littafin Attaura mai tsarki, da kuma tafsirinsa.

Sai dai kuma, ba duka matasan Haredi ne ke zuwa kwalejin addini ba, saboda haka sukan shiga soji da sharaɗin cewa za su dinga yin karatun addini.

Nahal Haredi sun fara aiki ne a matsayin ƙungiyar agaji a 1999, inda Yahudawan Haredi suka dinga shiga.

Sun yi aiki da ma'aikatar tsaro da kuma sojin Isra'ila don ɗaukar matasa Isra'ilawa da ba su zuwa makarantun addini.

Wannan haɗin gwiwar ne ya ba da damar kafa bataliyar Netzah Yehuda, inda ta ƙunshi dubban sojojin 'yan Haredi.

Wasu dakarun Netzah Yehuda suke fareti yayin rantsar da su a 2013

Asalin hoton, AFP / Getty Images

Bayanan hoto, Wasu dakarun Netzah Yehuda suke fareti yayin rantsar da su a 2013

Me ya sa Amurka ke son saka takunkumin?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An zargi dakarun Netzah Yehuda da kisan Bafalasɗine ɗan Amurka mai shekara 79, Omar Asaad a Janairun 2022, bayan an kama shi a kusa da wani wurin duba ababen hawa. Iyalinsa sun ce sojoji sun ɗaure hannayensa, suka rufe bakinsa kuma suka bar shi a ƙasa. An same shi babu rai kwance a ƙasa.

Bayan gudanar da bincike, rundunar sojin Isra'ila ta ce an samu "matsalar rashin tunani daga ɓangaren sojojin da kuma ƙarancin basirar yanke hukunci, abin da ya jawo cin zarafin rayuwar ɗan'adam".

Bayan faruwar lamarin, an dakatar da kwamandan bataliyar, aka cire kwamandojin tawagar amma kuma aka rufe maganar ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba.

Tun a ƙarshen 2022 ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fara bincike kan Netzah Yehuda bayan an zarge su cin zalin fararen hular Falasɗinawa. Bincken ya ƙunshi kisan Omar Asaad, kamar yadda jaridar Haaretz ta ruwaito.

Tun bayan ɓarkewar yaƙin Isra'ila a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba, Amurka ta saka takunkumai sau uku kan Yahudawan da suka kai wa Falasɗinawa hare-hare.

Tsohon sanatan jam'iyyar Democrat Patrick Leahy, shi ne ya jagoranci kafa dokar saka wa mutane takunkumi idan aka kama su da laifin cin zarafi ko take haƙƙin ɗan'adam

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon sanatan jam'iyyar Democrat Patrick Leahy, shi ne ya jagoranci kafa dokar saka wa mutane takunkumi idan aka kama su da laifin cin zarafi ko take haƙƙin ɗan'adam

Mece ce dokar Leahy da Amurka ke son yin amfani da ita kan bataliyar Netzah Yehuda

Dokar Leahy ta haramta bai wa wasu gwamnatoci tallafi waɗanda aka tabbatar sun take haƙƙiin ɗan'adam, a cewar ma'aikatar harkokin wajen Amurka.

Cikin abubuwan da ake haramtawa akwai ba da horo daga sojin Amurka.

Za a iya cigaba da bai wa ƙasa tallafi idan aka gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifi a gaban kotu.

BInciken da ake iya gudanarwa sun haɗa da siyasa, da tsaro, da kuma sauran haƙƙoƙin ɗan'adam.

Gwamnatin Amurka na ɗaukar "azabtarwa, da kisan mutane ba tare da haƙƙi ba, da tilasta wa mutane ɓuya, da fyaɗe" a matsayin manyan hanyoyin take haƙƙi.

Ana amfani da dokar ne idan aka tabbatar an aikata waɗannan laifukan.

Ana kiran dokar da suna Leahy ne saboda Sanata Patrick Leahy, wanda ya jagoranci kafa ta a shekarun 1990.