Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Balaraben Qatar ya ƙara tayi mai tsoka don sayen Man United
Sheikh Jassim bin Hamad Al Thani ya sake yin tayi mai tsoka domin sayen ƙumgiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United da ke Ingila.
Majiyoyi sun ce a ranar Talata Balaraben ya mika tayi a yayin da ake ci gaba da tattaunawa domin cefanar da kulob din.
Jassim da kuma Kamfanin Sir Jim Ratcliffe ne kan gaba a kokarin sayen kulob din mai wasa a Old Trafford.
Dukkansu sun mika tayi har sau uku a kan kulob din.
BBC ta fahimci cewa sabon tayin ya kunshi mallakar kungiyar gaba daya har da bashin da ake bin ta da kuma karin tallafin da za a bai wa mazauna yankin da kungiyar ta United take.
A cikin watan Maris, alkaluma sun nuna cewa ana bin United bashin kusan fan miliyan 967.
Iyalan Glazer sun sanar a cikin watan Nuwamba cewa suna duba yiwuwar sayar da Manchester United domin fuskantar wadansu abubuwan a nan gaba.
A shekara ta 2005 aka cefanar musu da United a kan fan miliyan 790 kuma darajar kungiyar ta kai tsakanin fan biliyan biyar zuwa shida.