Ko United za ta iya fitar da Sevilla a Europa a Sifaniya?

An wallafa

Kociyan Manchester United, Erik ten Hag ya bukaci 'yan wasa da su saka kwazo don kai wa daf da karshe Europa League ranar Alhamis.

Sevilla za ta karbi bakuncin United a wasa na biyu a quarter finals a Europa League da za su kece raini a Sifaniya.

A wasan farko da suka kara ranar Alhamis 13 ga watan Afirilu sun tashi 2-2 a Old Trafford, kuma United ce ta fara cin biyu daga baya aka farke su.

Sevilla ce kan gaba a yawan lashe Europa League mai shida jimilla, United daya ne da ita, wanda ta lashe a 2016/17 a lokacin Jose Mourinho.

Bayan da United ta fara zura kwallo biyu a ragar Sevilla, kungiyar Sifaniya ta farke sakamakon da Tyrell Malacia da kyaftin Harry Maguire suka ci gida.

Watakila wanda ke kan gaba a ci wa United kwallaye a bana, Marcus Rashford ya buga wasan, bayan da ya yi jinya.

Kociyan Sevilla, Jose Mendilibar ya ce Rashford yana da hadari idan yana taka leda, sai dai hakan ba zai daga musu hankali ba ko ya buga karawar.

Ranar Laraba Ten Hag ya sanar cewar Rashford ya yi atisaye tare da 'yan wasan United, amma kocin bai yanke hukuncin ko zai sa dan kwallon a karawa da Sevilla.

Rashford ya ci kwallo shida a Europa League a kakar nan, wanda yayi kan-kan-kan da Victor Boniface na Royale Union Saint Gilloise.

Sevilla ce ta hudu daga Sifaniya da United ke fuskanta a gasar ta zakarun Turai ta Europa League a kakar nan.

Tun farko United ta kara da Real Sociedad a cikin rukuni, inda kungiyar Sifaniya ta yi ta daya, United ta yi ta biyu.

Hakan ya sa kungiyar Old Trafford ta buga wasan cike gurbin zuwa zagaye na biyu a Europa League, wadda ta fitar da Barcelona.

A karawar zagaye na biyu kuwa, United ta yi waje da Real Betis.

Wasa tsakanin Sevilla da Manchester United:

Europa League Alhamis 13 ga watan Afirilun 2023

  • Man Utd 2 - 2 Sevilla

Europa League Lahadi 16 ga watan Agustan 2020

  • Sevilla 2 - 1 Man Utd

Champions League Talata 13 ga watan Maris 2018

  • Man Utd 1 - 2 Sevilla

Champions League Laraba 21 ga watan Fabrairun 2018

  • Sevilla 0 - 0 Man Utd