An dakatar da Ronaldo wasa biyu kan buga wayar dan kallo da kasa

An wallafa

An dakatar da Cristiano Ronaldo daga buga wasa biyu a cikin Ingila, sakamakon buga wayar dan kallo da kasa da ya yi a karawa da Everton.

Mai shekara 37, ya fasa wayar mai goyon bayan Everton a lokacin da za su koma dakin sauya kayan 'yan kwallo a Goodison Park cikin watan Afirilu.

Haka kuma hukumar kwallon kafar Ingila ta kuma ci tarar tsohon dan wasan Manchester United £50,000.

Hukuncin ba zai shafi wasannin da zai buga wa Portugal a Gasar Kofin Duniya a Qatar ba.

Zai yi wa Portugal kyaftin a rukuni na takwas a karawa da Ghana ranar Alhamis.

Hukuncin zai shafi dan kwallon idan zai buga wasa a Ingila a wata sabuwar kungiyar idan zai ci gaba da taka leda a can ko kuma a wata kasar.

Amma ba zai shafi wasannin Zakarun Turai ba.

Ronaldo da Manchester United sun amince sun raba gari a tsakaninsu, bayan wata hira da ya yi da Talk TV.