Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United ta kai daf da karshe a FA Cup na bana
Manchester United ta kai daf da karshe a FA Cup, bayan da ta doke Fulham 3-1 ranar Lahadi a Old Trafford.
Fulham ce ta fara cin kwallo ta hannun Aleksandar Mitrovic a minti na biyar da komawa zagaye na biyu.
United ta farke ta hannun Bruno Fernandes a bugun fenariti, bayan da Willian ya tare kwallo da hannu a lokacin da Sancho zai zare ta farko.
Hakan ya sa aka bai wa tsohon dan wasan Chelsea jan kati, bayan da alkalin wasa ya je ya duba na'urar da ke taimaka wa alkalin wasa yanke hukunci, wato VAR wadda ta fayyace masa komai.
Sai kuma aka bai wa Mitrovic jan kati, bayan da ya je yana kalubalantar alkalin wasa kan korar Willian da ya yi.
United ta kara na biyu ta hannun Marcel Sabitzer minti na biyu tsakanin da wadda United ta farke, sannan Fernandes ya kara na uku na biyu da ya zura a raga a wasan.
Da wannan sakamakon United za ta buga daf da karshe da Brighton ranar 23 ga watan Afirilu a Wembley.
Kafin nan Manchester City ce za ta fara fafatawa da Sheffield United a dai Wembley ranar 22 ga watan Afirilu.
United ta ci Fulham 2-1 a bana a Craven Cottage a gasar Premier League a kakar nan.
Kungiyar Old Trafford ta dauki Carabao Cup a kakar nan, bayan da ta ci Newcastle United a Wembley karon farko a kungiyar tun bayan 2007.
United tana zagayen daf da na kusa da na karshe a Europa League, wadda za ta kara da Sevilla gida da waje.
Haka kuma kungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama tana ta uku a teburin Premier League, mai fatan buga Champions League a badi.