Ko ƙirƙirarriyar mahaifaza ta taimaka wajen rage mutuwar bakwaini?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Jasmin Fox-Skelly
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Na'urorin goyon cikin na mahaifa da mabiyiya na iya ceton rayukan jariran da ba su isa haihuwa ba, amma me ya kamata a yi la'akari da shi kafin fara gwajin amfani da su don rayuwar ɗan'adam?
Ciro jarirai daga cikin mahaifar iyayensu tare da sanya su cikin na'urorin renon 'yan tayi, domin su ci gaba da rayuwa ya yi kama da almara.
Amma wannan shi ne haƙiƙanin abin da masana ke yi a asibitin yara na jihar Pennsylvania a Amurka ke shirin yi wa 'yan tayin da ke cikin hatsarin zubewar cikinsu kafin su isa haihuwa.
Suna ƙoƙarin samar da abin da suka kira ''ƙirƙirarriyar mahaifa'', ko wani sabon wuri da 'yan tayi ka iya rayuwa kafin su isa lokacin haihuwa.
Manufar shirin ba ita ce ƙara wa ɗan tayin girma daga lokacin ɗaukar ciki zuwa haihuwa ba - wannan ba zai yiwu ba koda ana son hakan. Madadin haka, an ƙirƙiri sabuwar mahaifar da nufin taimaka wa 'yan tayin su ci gaba da rayuwa waɗanda ke fuskantar barazanar lafiya da za ta iya shafar rayuwarsu.
A bisa al’ada, idan komai na tafiya daidai, goyon ciki na ƙarewa ne a mako 40, kodayake ana ɗaukar jararan da aka haifa a mako 37 a matsayin cikakkun jariran da suka isa haihuwa. To sai dai a wasu lokutan ana samun matsaloli a lokacin goyon ciki, lamarin da ke sa a haifi jararin kafin lokacin da ya kamata a haife su.
To amma wannan matsalar ta ragu cikin gomman shekaraun da suka shuɗe, bayan samun ci gaba a fannin lafiyar goyon ciki, lamarin da ya bayar da damar haifar jarirai ba tare da matsaloli masu yawa ba, koda kuwa ba su kai lokacin da ya kamata a haife su ba.
Alƙaluman baya-bayan nan sun nuna cewa kashi 30 na jariran da aka haifa a mako 22 za su iya rayuwa idan suka samu kulawar da ta dace.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"A Haƙiƙanin gaskiya 'yan tayi masu mako, 28 ko 27, ka iya rayuwa ba tare da wata matsala ba," in ji Stephanie Kukora, likitar jarirai a asibitin Mercy.
"Jariran da aka haifa a mako na 22 zuwa 23 ne ke cikin hatsarin rasa rayukansu, to sai dai ba mu sani ba yadda ake kula da su ɗin ya gaza abin da suke buƙata."
Jariran da aka haifa tskanin wannan lokaci kan zo da matsalolin da suka shafi lafiya.
Nauyinsu ba ya kai giram 900 a lokacin haihuwa, kuma muhimman gaɓoɓinsu kamar zuciya da huhu da ƙwaƙwalwa da ɓangaren da ke narkar da abinci ba su gama ginuwa ba, ta yadda za su ba su damar ci gaba da rayuwa, don haka dole ne sai an ba su kulawa.
Matsalolin da jarirai bakwaini suka fi fuskanta sun haɗa da matsalar hanji, lamarin da ke iya haifar da mutuwar jariri.
Haka jariran da aka haifa a wannan lokaci kan fusknaci matsalar kamuwa da cutuka, matsalar hawa ko sauƙar jini da zai iya lalata huhu da ƙoda da hanta da sauran sassan jiki.
Haka kuma ko da sun rayu akwai hatsarin su kamu da cutukan da za su jima suna fama da su, kamar cutukan da suka shafi ƙwaƙwalwa, lamarin da ka iya shafar koyon abubuwa da na gani ko matsalar ji da cutar asma.
Koda sabuwar fasahar da aka samar (Kwalba) don kare jariran, iskar oxygen da ake hura musu - ka iya yin illa ga huhunsu.
"A wannan lokacin huhun jariri bai kammala ginuwa ba," in ji George Mychaliska, Farfesa a fannin tiyata da ilimin lafiyar masu juna biyu da al'amuran da suka shafi mata a asibitin koyarwa na jami'ar Michigan.
"Amma lokacin da aka haife su a bakwaini, sai mu sanya wani bututun shaƙar iska a cikin moƙogoronsu don iskar oxygen ta samu damar shiga cikin huhunsu, kuma haƙiƙa wannan mun sani na haifar da wata matsalar.
Bayan wani lokacin hakan kan janyo cutukan da suka shafi huhu, lamarin da ka iya tsananta. Galibi jariran da aka sanya a cikin kwalba, bayan an fitar da su, sukan buƙaci samun wadatacciyar iska domin inganta lafiyarsu.
Haka wannan wadatacciyar iskar kan haifar da hatsarin samun makanta, saboda yadda iskar kan hure wa jariran idanu.
Haka kuma jijiyoyin da ke kai jini zuwa idanu galibi ba sa fara aiki sai dab da lokacin da jariri ya isa haihuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Yawan iskar Oxygen kan haifar da matsalar girma, haka kuma toshewar jijiyoyin jini kan haifar da matsalar gani.
Manufar samar da ƙirƙirarrun mahaifa da mabiyiya ita ce don taimaka wa huhun jariran, tare da bai wa jariran damar ci gaba da girma har zuwa lokacin da za su fara numfashi.
Masana kimiyya a asibitin koyarwa na CHOP, ƙarƙahsin jagoorancin Alan Flake, ƙwararren likitan 'yan tayi, suka yi wani shiri na samar da wata ƙirƙirarriyar mahaifa ko injin renon 'yan tayi da ke cike da wani ruwan sinadari mai kama da irin ruwan da ke cikin mahaifa.
Likitocin sun kuma yi ƙoƙarin haɗa ƙananan hanyoyin jinin jikin 'yan tayin da kuma na'urorin da ke jikin ƙirƙirarriyar mahaifar, domin samun damar tura jini cikin mahaifar har zuwa cikin zuciyar jaririn kamar dai yadda yake a cikin mahaifiyarsa.
A shekarar 2017 Alan Flake, da takwarorinsa, suka ɗauki jarirai takwas da aka haifa a mako 23 zuwa 24, domin saka su cikin ƙirƙirarriyar mahaifar. Kuma gwajin ya nuna cewa jariran sun ci gaba da girma ba tare da wata matsala ba.

Asalin hoton, Getty Images
Gwaji na biyu na baya-bayan nan da aka yi kan ƙirƙirarriyar mahaifar, shi ne wanda aka ajiye jarirai na tsawon kwanaki 16 kafin a mayar da su cikin kwalba, a wannan lokacin wasu sassan jikinta da suka haɗa da huhu za su ci gaba da girma.
Tawaga ta uku ta ƙwararru daga ƙasar Autraliya da Japan, na ƙoƙarin samar da ƙirƙirarriyar mahaifa da suka kira 'ex vivo', da nufin samun waraka daga cuutukan da jarirai bakwaini kan fuskanta, fiye da sauran gwaji biyun da aka yi a baya.
"A yanzu muna matakin da za muiya ɗaukar jararai masu nauyin giram 500, domin ci gaba da kula da su na tsawon mako biyu," in ji Matt Kemp, ƙwararriya a fannin goyon ciki da lalurorin mata a jami'ar Singapore, wadda ta jagoranci tawaga ta ukun.
"Wannan gagarumin ci gaba ne, to sai dai a ɗaya gefen girman waɗannan jarirai kan zo da matsaloli.
Mafi yawan gwaje-gwajen da aka yi kan ƙirƙirarriyar mahaifar an yi shi ne kan jariran da ba su da wata matsalar rashin lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Matsalar ita ce jaririn da aka haifa da wurwuri sakamakon wasu matsaloli, zai yi wahala ƙirƙirarriyar mahaifar ta iya magance matsalolinsu.
"A gwaje-gwajen da muka yi kan 'yan tayin da ke da matsaloli, akwai wahalar magance matsalolinsu," in ji Kemp.
"Ana samun gagarumar matsala wajen girmansu, da kuma gudanar jininsu, don hka abu ne da har yanzu muke zurfafa bincike a kai''.
Idan duka waɗannan gwaje-gwajen suka samu nasara, akwai yiwuwar samun nasara ko farin ciki ga iyayen da ke faɗawa naƙuda a lokacin da haihuwa ta zo musu kafin cikinsu ya kai lokacin haihuwa.










