Rashford ya kafa sabon tarihi a Man United

An wallafa

Marcus Rashford ya zama matashin da ya buga wa Manchester United wasa 250 a Premier League a karawa da Luton Town.

Ranar Asabar United ta doke Luton Town 1-0 a wasan mako na 12 a babbar gasar tamaula ta Ingila da suka kara a Old Trafford.

Rashford ya yi wannan bajintar kwana 11 da ya yi bikin zagayowar ranar da aka haife shi, ya kuma karbe gurbin da Ryan Giggs ya rike.

Giggs, tsohon dan kwallon tawagar Wales ya dade a matakin matashin da ya buga wa United tamaula da yawa, wanda ya lashe manyan kofuna a kungiyar.

Koda yake wasu sun ce Giggs ya buga wasanninsa tun daga karawar 'yan ajin rukuni farko zuwa lokacin da aka kirkiro Premier League.

Rashford, wanda ya fara United tun daga makarantar horar da tamaular kungiyar ya fara buga Premier a 2016 a wasan da ta doke Arsenal 3-2 a gida.

Ya fara yana da shekara 18, wanda ya ci Gunners kwallo biyu a ranar, sannan ya zura daya a ragar Midtylland a gasar Europa League, daga nan ya zama kashin bayan kungiyar.

Rashford, wanda ya buga wa United wasa 250 duk a Premier League tun da aka sauya fasalin gasar a 1992, ya ci kwallo 70.

Dan wasan tawagar Ingila ya karbi jan katin da aka yi masa a fafatawa da FC Copenhagen a Champions League, inda United take da maki uku a rukunin farko.