Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real za ta kara da Elche ranar 15 ga Fabrairu ko 8 ga Maris
Mahukuntan La Liga sun tsayar da ranar buga wasan mako na 21 tsakanin Real Madrid da Elche a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Za a buga fafatawar a Santiago Bernabeu ranar 15 ga watan Fabrairu ko kuma 8 ga watan Maris din 2023.
Real za ta fuskanci Elche ranar Laraba 15 ga watan Fabrairu, idan ba ta kai zagayen daf da karshe ba a Copa del Rey da za ta yi ranar Alhamis.
Ranar Alhamis 25 ga watan Janairu, Real Madrid za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a karawar daf da na kusa da na karshe.
Da zarar Real ta ci wasan watakila ta buga zagayen gaba na daf da karshe a kofin da Barcelona ko kuma Sevilla.
Idan ta kai daf da karshe a Copa del Rey kenan za ta fuskanci Elche ranar Laraba 8 ga watan Maris a mako na 21 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu.
Real Madrid wadda ta yi rashin nasara a hannun Barcelona da ci 3-1 a Saudi Arabia a Spanish Super Cup a Janairu tana ta biyu a La Liga da tazarar maki uku tsakaninta da kungiyar Nou Camp.
Barcelona ce kan gaba a yawan daukar Copa del Rey mai 31 jumulla, ita kuwa Real Madrid 19 ne da ita a tarihi.
Real Betis ce ke rike da kofin, wadda ta ci Valencia 5-4 a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1 a bara.