Mai fasa dutse da masallacin da ake sake wa yaɓe duk shekara na cikin hotunan Afirka

G

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mai sana'ar fasa dutse kenan ke gudanar da aikinsa ranar Asabar a garin Kajiado na arewacin ƙasar Kenya, Mutumin ya ce yakan samu dala 1.6 zuwa dala biyar a kowacce sa'a ɗaya
An wallafa
F

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Lahadi gwamman mutane sun taru domin yi wa wani daɗaɗɗen masallaci mai tarihi yaɓe a garin Djenne na ƙasar Mali.
S

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masallacin na ɗaya daga cikin manyan masallatai na duniya da aka gina da yumɓu da katako, kuma duk shekara ake sake yi masa yaɓe.
F

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Juma'a ne kuma uwar gidan shugaban Amurka, Jill Biden ta ziyarci babbar jami'ar Al-azhar da ke birnin Alqahira na ƙasar Masar, inda ta gana da shugaban jami'ar, Mohamed al-Mahrasawy...
X

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Lahadi kuma ta isa ƙasar Morocco a wani rangadin ƙasashen Afirka , inda ta gana da wasu ɗalibai da ke karanta fannin ƙera butum-butumi a wata makaranta da ke birnin Marrakesh mai dimbin tarihi
S

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Litinin kuma, aka ɗauki hoton wannan mutumin sanye da tufafin ledoji a ƙaras Ivory Coast, a ranar bikin kula da tsaftar muhalli ta duniya.
S

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Shi kuwa wannan mutumin kwashe sharar unguwarsu yake yi a birnin Nairobi na ƙasar Kenya albarkacin ranar tsaftar muhallin ta duniya da aka gudanar a cikin makon da ya gabata.
Z

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Alhamis kenan yayin da waɗannan matasan ke fita harkokin kasuwancinsu a birnin Khartoum na ƙasar Sudan, duk kuwa da yawaitar hare-hare ta sama da ake samu tsakanin ɓangarorin da ke faɗa da juna a ƙasar.