Yadda ƴan bindiga ke ƙona ƙauyuka ƙurmus a Darfur

Sama da mutane 90,000 ne suka tsere daga rikicin Darfur a kan iyakar kasar da Chadi, a cewar UNHCR

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Ƴan bindiga sun ƙona daukacin ƙauyukan yankin yammacin Darfur na ƙasar Sudan ƙurmus, inda a yanzu hukumomin agaji ke gargadin cewa al'ummar yankin na gab da faɗawa cikin mawuyacin hali.

Ƙazancewar matsalar sace-sacea da lalata muhimman ababen more rayuwa sun sanya mutane da dama ba su da isasshen abinci, babu ruwan sha mai tsafta, kuma babu magunguna.

Tsagaita wuta tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa-kai na Rapid Support Forces (RSF) ta haifar da sassauci a tashe-tashen hankula da ake samu kewayen birnin Khartoum na kasar Sudan.

Sai dai ana ci gaba da gwabza fada a yankin Darfur, kuma yayin da rikicin yankin ya shiga mako na bakwai, da alama yankin ya fada cikin rudani.

Waɗanda suka kasa tsere wa yaƙin sun yi ta tona ramuka a kewayen yankunansu tare da kafa shingaye domin hana mayakan sa-kai da ke lalata duk wani abu da ke hanyarsu, shiga.

Hotunan tauraron ɗan'adam da BBC ta samu sun tabbatar da cewa wani kauye da ke kusa da Nyala a Kudancin Darfur, Abu Adam, ya ƙone ƙurmus - za a iya ganin yadda wurin ya koma baƙi a cikin wannan hoto da aka ɗauka daga sararin samaniya.

...

Asalin hoton, Planet Labs PBC

Shi kansa garin na Nyala na fama da matsalar ƙarancin lantarki kuma yunƙurin tattaunawa da mutanen garin abu ne mai matuƙar wahala.

An katse hanyoyin sadarwa, amma na samu nasarar tattaunawa da wani ɗan jarida mai suna Essa Daffallah.

"Rundunar RSF ta afka cikin garin ɗauke da manyan motocin da ke dauke da bindigogi, da kuma babura masu yawan gaske," in ji shi, inda ya ƙara da cewa a ranar Juma'a 19 ga watan Mayu "an wawashe ofisoshi da shaguna masu zaman kansu".

"An yashe asibitin ne saboda yana cikin yankin da ake fada, an wawashe akasarin wuraren da ake haɗa magunguna, an rufe dukkan wuraren zama a Nyala gaba daya ta hanyar shingaye da tona ramuka, ta yadda mayakan ba za su iya shiga yankunan da ake zaune ba.

" Tuni dai wannan yankin ya kasance yana fafutukar taimaka wa dubban ɗaruruwan mutanen da wasu tashe-tashen hankula suka raba da muhallansu.

Wani mai raji a garin Nyala ya ce sama da mutane 600,000 da suka rasa matsugunansu, wadanda suka dogara gaba daya a kan taimako, ba su samu agaji ba tsawon kwanaki 40 saboda faɗan da ake yi.

...

Hotunan tauraron ɗan'adam sun ƙara nuna yadda hare-haren suka lalata muhimman abubuwan rayuwa da fafaren hula suka dogara da su, kamar babbar kasuwa -inda yake nuna cewa an ƙona ta.

Wannan babbar asara ce domin Nyala yana wadata yankin da ma wasu kasashe makwabta.

Jama'a na matukar bukatar taimako kuma ma'aikatan agaji suna ta kokarin shiga yankin. Sun taru a kasar Chadi da ke kusa da kasar tare da shirin tsallakawa zuwa yankin Darfur da zarar sun samu.

Hukumomin ba da agaji na taimakawa 'yan gudun hijirar da ke tsallakawa cikin kasar Chadi, amma sun kasa shiga Darfur saboda ci gaba da fadan da ake yi

Asalin hoton, Reuters

Justine Muzik Piquemal, daga wata ƙungiya bayar da agaji mai zaman kanta, mai suna 'Solidarites International' ta ce "Mun san cewa yana da matuƙar haɗari".

"Amma muna buƙatar aikawa da kayan taimako da wuri, domin idan ba haka ba, abin da za mu samu ina tsammanin gawarwaki ne a ko ina, ga shi kuma ana ƙarancin ruwa, babu banɗakuna kuma babu abincin."

Ms Piquemal ta shirya tallafin tan 13, wanda take fatan zai hada da tuƙa tankin ruwa zuwa birnin El Geneina, babban birnin yankin Darfur na yammacin Sudan.

...

Shekaru 20 da suka gabata, a lokacin yaƙin Darfur, tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir ya tara 'yan Janjaweed domin murƙushe tawayen ƙabilun da ba na Larabawa ba. An kashe dubban ɗaruruwan mutane. An zargi Janjaweed da aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil adama.

Yaƙe-yaƙen da ake yi a yanzu sun sake haifar da rikice-rikicen kabilanci.

"Matsalar ita ce ba bangarori biyu ne kawai suke fadan ba," in ji Konstantinos Psykakos, wani jami'in kungiyar Médecins Sans Frontières (MSF), wanda aka kai wa asibitinsa hari tare da yashe shi a El Geneina.