'Ba Buhari ne ya cire Osinbajo daga tawagar kamfe ɗin Tinubu ba'
An wallafa
Shirin Gane Mini Hanya na wannan makon ya karɓi baƙuncin Honarabul Abdulrahman Baffa Yola - mai bai wa Shugaban Najeriya Buhari shawara kan harkokin siyasa.
A hirar da Imam Saleh ya yi da shi, honarabul ɗin ya ce a tunaninsu ba Buhari ne ya ce a cire sunan Yemi Osinbajo daga tawagar kamfe ɗin Bola Tinubu ba, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC mai mulki.








