Man Utd na son musayar Rashford da Watkins, Man City na zawarcin Diogo Costa

Marcus Rashford

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marcus Rashford
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na duba yadda za ta yi musaya tsakaninta da Aston Villa inda ɗanwasan gabanta Marcus Rashford mai shekara 27, da ta ba da shi aro ya zama ɗanwasan dindindin a Aston Villa, amadadinsa kuma Aston Villa ta bai wa Manchester United ɗanwasanta Ollie Watkins mai shekara 29. (Star)

Mai tsaron ragar Kamaru Andre Onana mai shekara 29 zai samu damar barin Manchester United ne kawai idan har kulob ɗin ya samu tayin da ya zarce fam miliyan 20. (Mirror)

Kocin Atletico Madrid Diego Simeone na son ɗaukan ɗanwasan Argentina da Tottenham Cristian Romero kuma zai yi ƙoƙarin ƙulla yarjejeniya da ɗanwasan mai shekara 26 kafin gasar Club World Cup. (Sunday Express)

Ana alaƙanta ɗanwasan Sifaniya Nico Williams mai shekara 22 da komawa Arsenal da Barcelona amma ya nuna yana son ci gaba da zama a Athletic Bilbao don taka masu leda a gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa idan suka samu zuwa gasar. (AS - in Spanish)

Ana ganin ƙungiyoyi da dama na zawarcin ɗanwasan Sporting Gyokeres sai dai ɗanwasan mai shekara 26 ya ce "babu wanda zai iya hasashen abin da zai faru - muna jin daɗin yanayin da ake ciki". (Metro)

Real Madrid ta shirya raba gari da kocinta Carlo Ancelotti kuma ta tuntuɓi kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso duk da cewa darajarsa na iya kai wa kusan fam miliyan 15. (Sky Sports Germany)

Abin da Ancelotti yake so idan ya bar Real Madrid shi ne ya zama kocin tawagar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brazil. (Athletic - subscription required)

Ɗanwasan Sweden Alexander Isak wanda ake raɗe-raɗin Arsenal da Liverpool na zawarcin sa, ana sa ran zai ci gaba da zama a Newcastle United yayin da Magpies ke shirin taya ɗanwasan mai shekara 25. (Football Insider)

Chelsea da Newcastle da Juventus na zawarcin ɗanwasan Koriya ta Kudu Kim Min-jae yayin da Bayern Munich taka a shirye ta cefanar da ɗanwasan mai shekara 28. (Sky Sports Germany)

Manchester City na shirin ɗauko golan Porto Diogo Costa inda take tunanin tayin fam miliyan 50 kan ɗanwasan na Portugal ya wadatar. (Mirror)

Bayern Munich na bibiyar ɗanwasan Chelsea da Brazil Andrey Santos wanda yake zaman aro a kulob din Strasbourg na Faransa. (Mail)