Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
BBC ta samu damar ganin irin rawar da Amurka ta taka a hari kan Iran
- Marubuci, Jonathan Beale
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Defence correspondent
- Aiko rahoto daga, Buckley Space Force Base, Colorado
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
An bada umarnin "Lunch Yemen" wato a ƙaddamar wa Yemen kuma lokaci guda dukkanin sojojin da ke sanye da kaki mata da maza sun amsa da murya guda, "Copy, launch Yemen, wato "Mun ji, a ƙaddamar wa Yemen.
Dakarun sararin samaniyar Amurka, ba masu ɗaukan makamai ba ne. Aikinsu shi ne sanya ido a kan talabijin da ke haska musu sararin samaniya a wani yankin da ke Denver a jihar Colorado, suna iya gano daga inda aka harba makamai masu linzami daga ko ina a duniya - da kuma bibbiyar daga inda aka harbo da kuma ina suka dosa.
Mu ne ƴan jarida farko na duniya da aka ba wa damar shiga sansanin sojojin sararin samaniyar da ke bada gargaɗi da kuma sa ido da ke cikin wani ɗaki da ke sansanin na Buckley, ana aiki ba dare ba rana.
Suna zagaye da wasu manyan talabijin da ke ɗauke da bayanan taswira da aƙaluman da ake aiko musu da bayanan tsaro a kai a kai.
Waɗannan jami'an tsaro su ke soma samun ankararwa da zaran an harba makami mai linzami. Jim kaɗan aka jiyo - "Launch Iran" - wato a "ƙaddamarwa Iran".
Colonel Ann Hughes ta ce a shekarun baya-bayanan ayyuka na musu yawa, saboda yaƙi da ake yi daga kowanne ɓangare na gabas ta tsakiya da Turai.
Da muka tambayesu ko suna ankarar da Ukraine, Col Hughes ta ce: "Muna aika gargaɗi da ankarar da duk sojojin Amurka da abokan huldarsu. "Amurka ba zata fito ta tabbatar da hakan ba amma da alama tana sanar da Kyiv musamman lokacin da aka soma ƙaddamar ma ta hare-hare daga Rasha.
Waɗannan dakarun na Buckley za su kasance wani ɓangare mai muhimanci a shirin Donald Trump na samar da garkuwar kariya ga ƙasar Amurka daga makami mai linzami, da ake kira 'Golden Dome'.
Ya sanar da kashe dala biliyan 175 wajen tabbatar da shirin - wanda suke son yin koyi da shingen garkuwar sararin samaniyar Isra'ila na 'Iron Dome'. Mutane da dama dai na ganin za a kashe kuɗin da ya zarta hakan.
Laftanar Janar David Miller, wanda shi ne kwamandan dakarun sararin samaniyar Amurka ya ce samar da 'Golden Dome', na nuna yanayi na ƙaruwar barazanar tsaro da Amurka ke fuskanta.
Ya ambato China da Rasha.
Samar da wannan runduna ta tsaro shekaru biyar da suka gabata tabbaci ne cewa yaƙin ya koma sararin samaniya. Shugaba Trump a wa'adin mulkinsa na farko ya samar da wannan cibiya, yana mai bayyana sararin samaniya a matsayin sabon fagen yaƙi.
China da Rasha kowanne su sun yi gwajin wani tauraron ɗan adam da ke kakkabo makami mai linzami, da kuma hanyoyin katse layin sadarwa.
Janar Miller ya ce Rasha ta gwada ƙarfi da nuna alamun cewa tana iya samar da wata cibiyar jigbe makamin nukilliya a sararin samaniya.
A cibiyarsu da ke kusa da Colarado, tawagar na sa ido kan duk wani abu da ke tafe a duniya. Suna da tauraron ɗan adam dubu 12,000 a sararin samaniya. Kuma nan da shekara 10 ana sa ran za su bunƙasa su kai dubu 60,000.
Dakarun Amurka na cikin shirin ko-ta-kwana na yiwuwar ɓarkewar yaƙi a sararin samaniya. Kanal Hauser ta ce shekara guda da ta wuce ba sa iya magana kan ƙarfin ikonsu a sararin samaniya. Ta ce a yanzu, abin da suke fi mayar da hankali, shi ne tattara zaɓin da shugaban ƙasa ke da su wurin fahimtar hanyoyi mafi dacewa.
Janar Miller ya ce hanyar kare wannan yaƙi ita ce ta gwada ƙarfin iko kuma dole mu kasance muna da ƙarfin iya kare dukiyoyinmu". Amma ya ce ba zai bada bayanai kan abubuwan da ya ke nufi ba.
Amma hare-haren baya-bayanan na Amurka kan cibiyar nukiliyar Iran, wanda aka kira "Operation Midnight Hammer, ya ɗan nuna abin da dakarun sararin samaniyar Amurka za su iya yi.
BBC aka soma ba wa bayanan farko kan yadda dakarun sararin samanyar Amurka ke da hannu a waɗannan hare-hare.
Ƙwararru a harkar yaƙi ta amfani da na'ura daga cibiyar dakarun sa ido na sararin samaniya ta Delta 3 sun ce dama tuni suna aiki a wannan yanki.
Kwamandansu, Kanal Angelo Fernandez, ya nuna mun wani wuri da aka jero na'urorin da ke nuna taurarin ɗan adam da wurin da ake bada umarni, suna iya zuwa duk inda suke so a duniya.
Ya ce daga cikin wannan ɗaki ana iya kakkabo makamai da kuma yanke hanyar sadarwa tsakanin dakarun maƙiya juna.
"Suna iya kare dukiyoyin Amurka a kuma lokaci guda su yi tasiri a sararin samaniya da jirage ke kai komo," a cewarsa.
Kanal Phoenix ya ce sun yi ƙoƙarin amfani da naurorinsu wajen "fahimtar idan Iran ta san abin da ake kitsa ma ta, sannan suna da hanyoyin samun ankararwar cewa za a kai musu hari." Sun taimaka wajen kange Iran da ga samun bayanan fahimtar za a kai musu hari har zuwa lokacin da aka kammala komai.
Dakarun cibiyar kula da sararin samaniyar Amurka na iya kasancewa mafi kankantan shekaru da kafa su amma sun kasance masu ƙarfin faɗa a ji a ayyukan sojin Amurka. Janar Miller ya ce baki daya dakarun Amurka sun dogara ne kan wannan cibiya da ayyukan jami'anta.