Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan ƙungiyoyi na gogayya kan Greenwood, Madrid za ta sayi Gasiorowski
Barcelona da Atletico Madrid da Bayern Munich na daga cikin ƙungiyoyin da ke son ɗan gaban Marseille Mason Greenwood na Ingila mai shekara 22 (Talksport)
PSG ta dage kan son sayen ɗan gaban Newcastle Alexander Isak na Sweden mai shekara 24, wanda ƙungiyar tasa ta yi masa farashin kusan yuro miliyan 100 (Fichajes)
Nottingham Forest na sa ido sosai a kan ƴan wasan tawagar Turkiyya biyu ɗan gaba na gefe na Galatasaray Baris Alper Yilmaz, mai shekara 24, da kuma ɗan gaban Besiktas Semih Kilicsoy, mai shekara 19. (HITC)
Chelsea na son ta rabu da ɗan bayanta na Faransa Axel Disasi mai shekara 26 a lokacin kasuwar ƴan wasa ta Janairu. (Fichajes)
Arsenal ta gana da Ivan Toney na Ingila mai shekara 28, lokacin yana Brentford, amma kuma ƙungiyar ta fasa sayen ɗan gaban, inda daga bisani ya tafi Al-Ahli ta Saudiyya. (TBR Football)
Real Madrid na duba yuwuwar biyan yuro miliyan 45 na yarjejeniyar sayen matashin ɗan bayan Valencia Yarek Gasiorowski na Sifaniya. (AS)
Everton za ta bai wa ɗan gabanta Dominic Calvert-Lewin, na Ingila dama ta ƙarshe ta ƙulla sabon kwantiragi kafin kwantiraginsa na yanzu ya ƙare a bazara ta gaba, amma kuma Newcastle na nuna sha'awarta a kan ɗan wasan mai shekara 27. (Teamtalk)
Juventus za ta nemi sayen ɗan gaban Lille na Kanada Jonathan David mai shekara 24 a watan Janairu a kan yuro miliyan 15. (Calciomercato)
An kasa cimma yarjejeniya tsakanin ɗan bayan Southampton da Ingila Kyle Walker-Peters, wanda kwantiraginsa na yanzu zai ƙare a bazara mai zuwa. (Fabrizio Romano)
Southampton na sanya sunan kociyan Blackburn John Eustace a ƙoƙarin da take yi na neman wanda zai maye gurbin Russell Martin. (Football Insider)