Postecoglou ya buƙaci a bai wa Solanke lokaci

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ange Postecoglou ya ce Tottenham ta yi nazarin sayen Ivan Toney a kafin ta ɗauki Dominic Solanke, ya kuma yi kira ga magoya bayan ƙungiyar da kada su yi gaggawar yanke hukunci kan ɗan wasan da aka kashe fam miliyan 65 a kansa.

Solanke, mai shekara 27, har yanzu bai ci wa Spurs ƙwallo ba a wasanni uku da ya buga a bana tun lokacin da ya koma arewacin Landan daga Bournemouth a watan Agusta.

Ɗan wasan Ingila Toney daga ƙarshe ya koma ƙungiyar Al-Ahli ta ƙasar Saudiyya daga Brentford kan kuɗi fan miliyan 40 a ranar da aka rufe kasuwar musayar ƴan wasa ta bana.

Spurs dai ta samu nasara a wasa ɗaya ne kacal cikin guda huɗun da ta buga a gasar Premier bana sannan kuma za ta karɓi baƙuncin Brentford ranar Asabar.

"Mun yi nazari a kan shi [Toney] amma Dom shi ne wanda muke so wanda ya dace da ɗan wasan da muke nema a lokacin," in ji Postecoglou.

Kuma kocin Spurs din ya jaddada cewa rashin zura ƙwallo a raga da Solanke ya yi a wasanni biyu na farko na gasar Premier ba wani abin tashin hankali ba ne.

"Bai kamata mu yi gaggawar yanke hukunci ba a kodayaushe domin akasin haka shi ne watakila ya fara taka leda cikin sa'a, ya kasance da koshin lafiya, ya kuma zura ƙwallo a raga a dukkan wasanni huɗu, sai daga baya kuma ya fara samun rashin tagomashi kamar yadda mafi yawan ƴan wasan gaba ke samu.''

Tottenham tana matsayi na 13 a teburin Premier bana inda take da maki huɗu cikin wasannni huɗun da ta fafata a farkon kakar wasan bana kuma rahotanni na cewa magoya bayan ƙungiyar sun fara gunaguni kan rashin fara kakar bana da ƙafar dama inda suke ganin ya kamata Solanke ya fi haka ƙokari bisa la'akari da irin kuɗin da aka kashe wurin ɗauko shi.