Ko shan Paracetamol na da haɗari ga masu juna-biyu?

    • Marubuci, Andre Biernath & Sarah Bell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Brasil & World Service Global Health
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Gwamnatin Donald Trump tana yunƙurin alaƙanta shan paracetamol da masu juna-biyu ke a yi a ƙasar da kamuwa da cutar matsalar ƙwaƙwalwa ta yara wato autism, kamar yadda kafofin sadarwa na Amurka duka ruwaito.

A ranar Juma'a da ta gabata ce shugaban ya yi jawabi game da cutar, inda ya ce ta fara wuce yawaita a ƙasar, "don haka dole mu ɗauki mataki bayan gano musabbinsa."

Wasu bincike da aka gudanar sun alaƙanta shan sinadarin acetaminophen - wanda shi ne asalin sinadarin da ke cikin Tylenol ko kuma Paracetamol - da kamuwa da cutar ta kwakwalwa, amma binciken ba su fayyace alaƙar ba, da kuma irin illar da maganin ke yi.

Me ya sa sinadarin Paracetamol?

Paracetamol ko kuma Tylenol magani ne da za a iya saya a wuraren sayar da maganguna domin rage raɗaɗi, kuma asalin sinadarin da ke cikinsa shi ne acetaminophen a Amurka, ko kuma paracetamol a wasu wuraren.

Ana sayar da shi da suna daban-daban kuma akwai nau'uka da dama domin amfanin jarirai da ƙananan yara, kuma magani ne da ya yi fice wajen rage raɗaɗi.

Barazana ga masu juna-biyu

Manyan ƙungiyoyin lafiya da gwamnatoci a ƙasashen duniya sun ce babu wata barazana da masu juna-biyu ke fuskanta game da shan maganin.

Kwalejin kula da masu juna-biyu a Amurka wato American College of Obstetrics and Gynecology ta ce likitocin ƙasar sun tabbatar da cewa paracetamol na cikin maganganun rage raɗaɗi da ba su da wata barazana ga masu juna-biyu.

Haka kuma cibiyar lafiya ta Birtaniya wato UK National Health Service ta bayyana cewa paracetamol ne zaɓin farko ga masu juna-biyu, kuma babu wata illa a amfani da shi.

Kamfanin Kenvue mai haɗa Tylenos ya kare amfani da maganin ga masu juna-biyu, inda ya ƙara da cewa magani ne amintacce.

BBC ta tuntuɓi kamfanin, inda shi da likitocin Amurka suka shawarci mata su riƙa neman shawarar likitoci kafin amfani da maganin.

Kafofin sadarwa a Amurka sun ruwaito cewa gwamnatin Trump ta shawarci mutane su riƙa amfani da maganin ne kawai idan zazzaɓi ya yi tsanani.

Shin Tylenol na jawo cutar ƙwaƙwalwa?

A watan Afrilu, shugaban sashen kula da lafiya na Amurka Robert F Kennedy Jr ya sha alwashin cewa za su yi bincike domin gano asalin musabbanin cutar kwakwalwar ta autism a cikin wata biyar.

Sai dai masana sun yi gargaɗin cewa gano asalin musabbin cutar ba abu ba ne mai sauƙi, ganin an sha gudanar da binciken a gomman shekarun da suka gabata.

Masana da dama sun ce babu abu ɗaya tilo da za a ce shi ne yake janyo cutar.

A watan Agusta, nazarin wani bincike da shugaban tsangayar kwalejin kiwon lafiya na Jami'ar Oxford ya jagoranta, ya gano cewa yara za su iya kamuwa da cutar da wasu na'ukan cututtuka masu wahalar sha'ani idan ana shan paracetamol a lokacin da ake ɗauke da juna-biyunsu.

Binciken ya ƙara da cewa akwai buƙatar a rage shan maganin, amma suka ƙara da cewa ana buƙatar maganin domin rage raɗaɗi.

Amma a wani bincike da aka yi a shekarar 2024, ya gano cewa babu wata alaƙa tsakanin paracetamol da cutar autis.

Yadda Tylenol ke aiki

Magungunan rage raɗaɗi da ake kira analgesics kala biyu ne da ake kira opioids ko dai non-opioids.

Opioids shi ne wanda ake haɗawa daga tsirrai a ɗakunan gwaje-gwaje da suke aiki da sinadaran opioid da ke cikin ƙwaƙwalwa, wanda kuma ke fitar da sinadarin dopamine, wanda shi ne ke da alaƙa da samun natsuwa.

Amma sai dai maganin yana da saurin sabo da yanayin jikin mutum, wanda hakan ya sa masana suka ce zai fi kyau a fara amfani da magani mara ƙarfi zuwa mai ƙarfi, wato daga na'u'in non-opioids irin paracetamol domin rage raɗaɗin.

Amma har yanzu babu cikakken bayani kan yadda paracetamol ke aiki a jikin mutum.

Hukumar lafiya ta Birtaniya ta ce paracetamol na aiki ne ta hanyar tare wasu sinadarai ƴan aike a cikin ƙwaƙwalwa da suke isar da saƙon raɗaɗi da rage zafin jiki.

Akwai kuma wani bayanin da ke cewa paracetamol na aiki ne ta hanyar hana sinadarin sauƙaƙa aiki a jikin mutum mai suna cyclooxygenase ko kuma COX wanda ke fitar da sinadarin prostaglandins da ke da alaƙa da raɗaɗi aiki, wanda hakan ke jawo ragowar raɗaɗin.

Yawan Tylenol da ya kamata a sha

Masana kiwon lafiya sun ce akwai buƙatar a riƙa kula sosai wajen amfani da paracetamol.

Sun ce ba shi da wani matsala idan aka kiyaye dokokin amfani da shi, kuma idan ba a daɗe ana ta'ammali da shi ba.

Ƙa'idar amfani da shi, shi ne kamar yadda hukumar lafiya ta Birtaniya ta ce, a sha ɗaya ko biyu masu nauyin 500mg, ko kuma zuwa sau huɗu a rana amma kar ya wuce guda takwas a rana.

Wuce wannan ƙa'idar zai iya shafar hanta domin bincike ya gano cewa kashi 5 na paracetamol yake narkewa ya zama cuta.

Alƙaluma daga hukumar kula da ingancin abinci da magunguna na Amurka sun nuna cewa wuce ƙa'idar shan paracetamol ne kan gaba wajen jawo cutar hanta a Amurka a tsakanin 1998 da 2003.

Haka kuma masana sun gargaɗi iyaye da su sa ido kan yaransu wajen amfani da maganin.

Ƙarfin paracetamol

Hukumar lafiya ta duniya ta sahale amfani da paracetamol a matsayin maganin farko domin rage raɗaɗi da zazzaɓi wanda bai yi zafi ba.

Idan bai yi aiki ba, ana shawarartar masu jin raɗaɗin su ƙara gaba kaɗan su yi amfani da opioids marasa ƙarfi, sai a je kan masu ƙarfi, idan ba su yi ba sai a kai ga ganin ƙwararren likita.

Ƙarfin paracetamol ya daganta ne da irin zafin zazzaɓin.