Ta yaya rikicin kasuwancin Amurka da China zai shafi Afirka?

    • Marubuci, Nkechi Ogbonna
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, West Africa correspondent
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauki matakansa na farko waɗanda mutane da dama ke kallo a matsayin ɗan-ba na ɗaya daga cikin rikice-rikicen kasuwanci mafi girma tsakanin ƙasar da ƙasashen da take cinikayya da su.

Duk da cewa Trump ya jinkirta ƙudurinsa na lafta haraji kan kayan da ake ƙerawa a Mexico da Canada, matakin da ya ɗauka na lafta harajin kashi 10% kan kayan da China ke ƙerawa ya riga ya fara aiki.

Inda wasu ke kallon lamarin a matsayin wata ƙofa ta buɗe gagarumar rikita-rikitar kasuwanci a duniya, tuni masana suka fara nazari kan tasirin da matakin - wanda zai iya janyo taɓarɓarewar kasuwanci a duniya - zai yi ga ƙasashen nahiyar Afirka.

Najeriya, Kenya, Ghana, Angola da Afirka ta Kudu na daga cikin ƙasashen da ke gaba-gaba a nahiyar Afirka wajen cinikayya da Amurka.

Bayanai daga ofishin kula da lamurran kasuwanci na Amurka, a shekarar 2022, ya nuna cewa Amurka ta karɓi kaya daga Afirka ta Kudu waɗanda kuɗinsu ya kai dala biliyan 14.6, waɗanda suka haɗa kayan ado da duwatsu masu daraja da kuma ƙarafa.

Ta kuma sayi wasu kayan kamar zinare da ƴaƴan cocoa da sinadarin uranium da tasa da ƙarafa da wasu da dama daga ƙasashen Afirka irin Ghana, Ivory Coast, Gambiya da kuma Senegal.

Har ila yau a shekarar ta 2022, Najeriya - ƙasar da ta fi kowacce ƙasa a Afrika yawan al'umma - ta fitar da kaya da kuɗinsu ya kai dala biliyan 4.8 zuwa Amurka, waɗanda su ka haɗa da ɗanyen mai, ƴaƴan Cocoa, kayan abinci da sauransu, yayin da ta shigo da motoci da injina da kuma tattacen mai daga Amurkar.

Wannan cinikayya za ta iya raguwa sosai idan har harajin da Trump ke sanyawa ya iso kan abokan cinikayyarsu na Afirka.

Ƙasashen Afirka na cigaba da amfana da yarjejeniyar ƙudirin bunƙasa Afirka da samar da damarmaki (AGOA); wata dokar cinikayya ta Amurka da ke bai wa ƙasashen kudu da hamadar sahara da suka cancanta damar shigar da kaya Amurka ba tare da biyan haraji ba.

Dokar wadda Shugaba Bill Clinton ya sanya wa hannu a 2000 an sabunta ta, na baya bayanan shi ne aka yi a shekarar 2015.

Dokar za ta ƙare a Satumban 2025, kuma ƙudirin sabunta ta da aka yi a 2024 da ke so a tsawaita yarjejeniyar zuwa 2041 bai samu amincewa ba har tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya sauka.

Ana samun fargaba tsakanin wasu a Afirka cewa ba lallai Shugaba Trump ya goyi bayan sabunta dokar ba a cikin tsare-tsarensa na tattalin arziƙi na sanya buƙatun Amurka a farko.

''Da zarar an fara sanya haraji bayan ƙarewar AGOA, ƙanana da matsakaitan ƴan kasuwa a Afirka za su sha wahala.'' kamar yadda Obiora Madu, shugaban cibiyar hada-hadar kaya ta Afirka ya shaida wa BBC.

A yanzu haka dokar AGOA ta bai wa ƙasashe 32 da suka cike ƙa'ida damar shigar da kaya, akasari kayan abinci, fata, sinadarai, tsumin ƴaƴan itatuwa, ƙarafa da sauransu.

Durƙushewar tattalin arziƙin da ake hasashe zai iya kaiwa ga raguwar tattalin arzikin cikin gida (GDP) a ƙasashen Afirka.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi hasashen ƙaruwar GDP din zuwa kashi 3.7 cikin ɗari a 2025, daga kashi 3.4 a 2024, yayin da Bankin Bunƙasa Afirka ya yi hasashen ƙarin kashi 4.2 cikin ɗari a wannan shekarar, daga kashi 3.8 a bara.

Raguwar cinikayyar zai kai ga raguwar bunƙasar tattalin arziƙin.

Masu fashin baƙi na kuma cigaba da tantance irin tasirin da girgizar tattalin arziƙin China sakamakon ƙarin harajin da Trump ya yi zai yi wa Afirka.

China ta sanar da matakan martani da ta ɗauka kan matakin shugaban Trump inda ta ce za ta sanya harajin kashi 15 cikin 100 kan makamashin kwal da iskar gas da kuma motocin da za a shigar daga Amurkar. Ƙasar ta kuma bayyana aniyarta ta shigar da ƙorafi a ƙungiyar cinikayya ta duniya.

A shekarun baya-baya, China ta ƙara faɗaɗa alaƙar kasuwancita a Afirka, inda ta ke neman zama babbar abokiyar cinikayyar Nahiyar ganin cewa kasuwanci tsakanin yankunan biyu ya kai dala biliyan 282 a 2023, yawan da ba a taɓa gani ba.

China na shigar da kayyayaki kamar ma'adinai da makamashi daga Afirka, yayin da take fitar da kayyakin da aka sarrafa zuwa nahiyar.

Najeriya ta cigaba da kasancewa kasuwa mafi girma na kayyaykin China a Afirka inda ake samun fargabar shamaki ga kasuwannin Amurka zai tilastawa China cika kasuwannin Afirka da kayanta.

''China za ta iya fara cika Nahiyar da kayyayakinta, ta mayar da Afirka inda zata rinka jibga kayyakinta wanda kuma zai zama barazana ga masu sarrafa kayyayki na Nahiyar. Dele Ayemibo, kwararre a fannin cinikayya ya shaidawa BBC.

Wasu ƙasashen Afirka sun daɗe suna fama da shigowar kayyayaki marasa inganci daga Asiya, duk da ƙoƙarin da hukumomin kula da hakan keyi, Nahiyar na cigaba da tafka asara sakamakon hakan.

Ƙungiyoyin kamfanoni masu zaman kansu da dama sun buƙaci gwamnatocin Afirka su yi amfani da yaƙin kasuwancin da akeyi su duba cikin Nahiyar su karfafawa masu sarrafa kaya na cikin gida, ta hanya bunƙasa darajar kayyayakin da ake samu da kuma bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasashen.

Yarjejeniyar yin kasuwanci ba tare da shinge ba tsakanin ƙasashen nahiyar Afirka, AfCFTA, bai cika muradun sa ba tun bayan amincewa da shi shekaru biya da suka gabata.

Rashin kayyakin aiki, shingen kasuwanci, rashin hanyoyi masu kyau, da rashin kyaun iyakoki sun kawo tsaiko wajen aiwatar da yarjejeniyar da ke buƙatar zuba hannun jarin biliyoyi kafin fara aiki yadda ya kamata.

" Ƙasashen Afirka su ƙara tasirin AfCFTA. Su na buƙatar su ƙara yawan kasuwanci tsakaninsu su tabbatar yarjejniyar ta yi aiki.'' inji Obiora Madu.

Ƙawancen ƙasashe da dama wanda Brazil da Rasha da Indiya da China da Afirka ta kudu suka kafa da ake kira BRICS na da nufin bunƙasa alaƙar tattalin arziƙin ƙasashen ya kuma rage tasirin dalar Amurka a matsayin kuɗin da aka fi cinikayya da shi.

Wasu ƙasashen Afirka da aka amince su shiga ƙawancen sun haɗa da Masar da Habasha da Najeriya da Aljeriya da Uganda.

A makon da ya gabata, Shugaba Donald Trump ya gargaɗi ƙasashen BRICS da su kauracewa maye gurbin dala a matsayin kuɗin hada hada, inda ya nanata barazanarsa na sanya harajin kashi 100% wanda ya ambata makonni bayan lashe zaɓen shugaban ƙasa a watan Nuwamba.

'' Za mu buƙaci waɗannan ƙasashen waɗanda ke adawa da mu su tabbatar mana cewa ba za su ƙirƙiri wani kuɗi na ƙungiyar BRICS ba kuma ba za su goya ma wata takardar kuɗi baya domin ta maye gurbin dalar Amurka a harkar kasuwanci ba, in ba haka ba za su fuskanci haraji da kashi 100%, inji Trump a shafinsa na Truth.

'' Babu wata dama da BRICS za ta maye gurbin dalar Amurka a kasuwar duniya, ko a wani wuri ma, kuma duk wata ƙasa da ta yi yunƙurin haka to ta yi maraba da haraji, ta kuma yi bankwana da Amurka.'' inji shi.

Ƙasashen Afirka na da yiwuwar fuskantar samun raguwar kuɗaɗen shiga daga ƙasashen waje saboda ƙarin kuɗin ruwa da Amurka tayi a ƙoƙarin rage hauhawar farashi.

Ƙuɗaɗe kamar su Naira na Najeriya, da Rand na Afirka ta kudu, da Shilling na Kenya na iya fuskantar matsi, wanda zai iya ƙara rage ƙarfi da darajarsu.

Yaƙin kasuwancin ya kuma bayar da dama ga ƙasashen Afirka.

A yayin da ake ganin babu makawa za a samu targarda a inda ake samo kayyayki na duniya, ƙasashen masu ƙarfin tattalin arziki za su iya sauya hanya ta hanyar kai kayyaykinsu zuwa Amurka ta Afirka, da kuma samo kayyayaki zuwa ƙasashensu daga Amurka ta Afirka, wanda hakan zai baiwa Nahiyar damar samar da sabbin haɗaka da bunƙasa fitar da kaya.

Sai dai gwagwarmayar da ƙasashen masu tasowa ke cigaba da fuskanta na zama tangarda da ke toshe damar da za su samu a tsaka da yaƙin kasuwanci tsakanin ƙasashen masu ƙarfin tattalin arziƙi, wanda hakan zai hana su amfana.

"Afirka za ta amfana da wannan yaƙin kasuwancinne idan ta farga ta magance matsalolin gudanarwar ta.'' inji Mista Ayemibo.