Mbappe ya kai Real matakin farko a teburin La Liga

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kylian Mbappe ya kai Real Madrid matakin farko a teburin La Liga, sakamakon da ya ci Villareal ƙwallo biyu ranar Asabar a Estadio de la Ceramica.

Villareal ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Juan Foyth a minti na bakwai da fara wasan, daga baya Kylian Mbappe ya farke minti 10 tsakani, sannan ya ci na biyu a wasan.

Kawo yanzu Mbappe ya zura ƙwallo 20 a raga a La Liga, yana da tazarar ɗaya tsakani da Robert Lewandowski, wanda shi ne kan gaba a cin ƙwallaye a raga.

Hakan ya sa Real Madrid ta hau kan teburi La Liga da tazarar maki uku tsakani da Barcelona wadda ta koma ta biyu.

Ranar Lahadi Barcelona za ta je gidan Atletico Madrid a wasan mako na 28 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Villareal ta ci gaba da zama mataki na biyar da tazarar maki biyar tsakani da gurbin masu buga Champions League a baɗi daga Sifaniya idan an kammala gasar a haka.

A kakar bana Real ce ta doke Villareal 2-0 a Santiago Bernabeu ranar 5 ga watan Oktoban 2024.

Rabon da Real ta yi nasara a gidan Villareal a La Liga tun 2017, amma Real ta yi nasara a gidan Villareal 3-2 a Copa del Rey ranar 19 ga watan Janairun 2023.

Ƴan wasan Real Madrid da aka je da su Villareal ranar Asabar.

Ƴan wasan Real Madrid:

Masu tsare raga: Courtois, Lunin and Fran González.

Masu tsare baya: Alaba, Lucas V., Fran García, Rüdiger, Asencio, Diego Aguado and Valdepeñas.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni and Arda Güler.

Masu cin ƙwallaye : Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick and Brahim.