Za mu kori duk wanda ya yi cuwa-cuwar takarda daga aiki, idan ya ga dama ya zaɓi Fir’auna - Radda

Asalin hoton, Dikko Radda/FB
Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ya sha alwashin sallamar duk wani ma'aikaci da aka samu ya na amfani da takardun bogi.
Gwamnan ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi a wajen wani taro da ya gudana a jihar, inda ya ce idan aka bar irin waɗannan ma'aikatan, musamman a fannin ilimi, za a ɓata jihar da mayar da ita baya.
Ya ce ba zai ɗaga ƙafa wajen aiwatar da wannan mataki ba, ko da mutum zai "zaɓi Fir'auna" ne a madadinsa.
"Wanda ya yi cuwa-cuwar takarda aka ɗauke shi aiki, ba shi ba aiki...siyasa kuma idan ya ga dama ya je ya zaɓi Fir'auna," in ji Gwamna Radda.
"In ba da ka da takarda aka kore ka aiki sai me?...ko gobe muka kama wanda ba shi da takarda korar shi za mu yi".
Cikin wani gajeren bidiyo da Katsina Post ta wallafa a shafin Facebook, Radda ya mayar da martani kan abin da ya kira "siyasantar da sha'anin ilimi" da wasu ke yi a jihar.
Kalamansa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙorafi kan abin da suka bayyana yawan gudanar da ayyukan tantance ma'akata a jihar tun bayan hawan gwamnan.



























