Salah ya tsawaita zamansa a Liverpool da shekara biyu

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Masar, Mohamed Salah ya sanya hannu kan ƙarin kwantiragin shekara biyu da Liverpool.

Tsohon ƙwantiragin ɗan wasan zai ƙare ne a ƙarshen kakar wasa da muke ciki.

An dai riƙa samun shakku kan ko zai ci gaba da zama a ƙungiyar bayan wasu kalamai da ya yi a a farkon kakar nan, inda aka riƙa alaƙanta shi da ƙungiyoyin Saudiyya.

To sai dai yanzu ɗan wasan zai samu damar ƙara yawan ƙwallo 243 da 109 da ya bayar aka zura a cikin wasa 393 da ya yi wa ƙungiyar.

"Tabbas na yi farin ciki - a yanzu muna da ƙungiya mai ƙarfi," in ji Salah.

"Ƙungiyarmu na da ƙarfi tun a baya, Amma na tsawaita zamana ne saboda ina tunanin muna da damar lashe wasu ƙarin kofuna a nan gaba....''.

"Na yi shekara takwas a nan, ina fatan su kai 10. Ina jin daɗin rayuwa a nan, da jin daɗin wasana. Na samu shekaru mafiya daraja a rayuwar sana'ata a nan.''

Salah ya ci ƙwallo 32 a duka wasannin da ya buga a kakar bana, ciki har da 27 da ya zura a Gasar Premier yayin da Liverpool ke dab da lashe kofin gasar ta bana.

A yanzu haka ƙungiyar ce ke jan ragamar teburin Gasar Premier da tazarar maki 11 tsakaninta da Arsenal ta biyu, yayin da ya rage wasa bakwai a ƙarƙare gasar.

A shekarar 2017 ne Salah ya koma Anfield daga Roma, inda ya taimaka wa ƙungiyar lashe Kofin Zakarun Turai da na Premier League da kofin FA da na League Cup da kuma Kofin Gasar ƙungiyoyi ta Nahiyoyi.

Tsohon kwantiragin Salah ya ƙunshi biyansa fiye da fam 350,000 a kowane mako, lamarin da ya sa ya zama ɗan wasan da aka fi biya a tarihin ƙungiyar.

An kuma fahimci cewa sabon kwantiragin bai tanadi rage masa albashin ba.

Ya kasance ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan Liverpool uku da kwantiraginsu ke ƙarewa a bana, ciki har da ƴan wasan bayan ƙungiyar, Trent Alexander-Arnold da Virgil van Dijk.