Man City na zawarcin Wirtz don maye gurbin Bruyne, Liverpool na bibiyar Yamal

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na zawarcin ɗanwasan Bayer Leverkusen Florian Wirtz mai shekara 21 wanda take tunanin ya maye gurbin ɗanwasan tsakiya na Belgium Kevin de Bruyne da zai bar kungiyar. (Fabrizio Romano)
Manchester United da Nottingham Forest da Bayern Munich sun zaƙu kan ɗaukan ɗanwasan Faransa Jean-Philippe Mateta, 27 daga Crystal Palace a wannan bazarar. (Teamtalk)
Chelsea ta karfafa wa Aston Villa gwiwa kan yarjejeniyar ɗaukan ɗanwasan Ingila mai shekara 23 Noni Madueke, duk da cewa ɗanwasan bai ji daɗin rashin samun lokacin buga wasa a Stamford Bridge ba. (Football Insider)
Wakilin ɗanwasan Sporting Viktor Gyokeres zai kasance a wasan da Arsenal za ta buga da Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai, abin da ya ƙara rura wutar jita-jitar cewa ɗanwasan Sweden mai shekara 26 na shirin komawa Gunners. (Football Transfers)
Liverpool da Manchester City na bibiyar yadda lamari ke kasancewa ga kwangilar ɗanwasan gaba na Barcelona Lamine Yamal amma ɗanwasan mai shekara 17 a shirye yake ya ci gaba da zama a ƙungiyar. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Barcelona na iya amincewa da yarjejeniyar musayar ɗanwasa Ronald Araujo mai shekara 26 da ɗanwasan Liverpool mai shekara 28 Luis Diaz. (Relevo - in Spanish)
Manchester City na fatan ɗaukan ɗanwasan Aston Villa Morgan Rogers mai shekara 22 kasancewar Pep Guardiola ya kasance mai sha'awar salon wasan ɗanwasan na Ingila wanda a baya ya kasance a makarantar horas da ƴanwasa ta City. (Teamtalk)
Shawarar Alejandro Garnacho na saka gidansa a kasuwa ba wai saboda ɗanwasan na Argentina mai shekara 20 yana shirin barin Manchester United ba ne. (Mirror)










