An raba katin gargaɗi da yawa a tarihi a wasan Bournemouth da Chelsea

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ranar Asabar aka kafa tarihin yawan bayar da katin gargaɗi a gasar Premier League a wasan Bournemouth da Chelsea.

Ƙungiyar Stamford Bridge ce ta yi nasara da cin 1-0 ta hannun Christopher Nkunku a wasan na mako na huɗu a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Alkalin wasa Anthony Taylor ne ya busa karawar, wanda ya bayar da katin gargaɗi 14 tsakanin ƴan wasan ƙungiyoyin biyu a wasan da aka yi a filin Vitality.

Taylor ya raba kati mai ruwan ɗorawa 14 a ƙeta 25 da aka yi, shi ne wasan da aka fi bayar da katin gargaɗi mafi yawa a tarihin Premier League.

An bai wa ƴan wasan Bournemouth kati mai ruwan ɗorawa shida, yayin da aka bai wa na Chelsea guda takwas.

Mai masaukin baƙi ta samu bugun fenariti tun kan hutu, inda aka bai wa mai tsaron ragar Chelsea, Robert Sanchez katin gargaɗi.

Haka kuma an bai wa mai horar da Bournemouth, Andoni Iraola da na Chelsea, Enzo Maresca kati mai ruwan ɗorawa, koda yake baya cikin lissafin 14 da aka bai wa ƴan wasan.

A bara ne aka bayar da katin gargadi 13 a Premier League a wasan da Tottenham ta doke Sheffield United 2-1

A kakar 2016 an raba kati mai ruwan ɗorawa 12 a wasa tsakanin Chelsea da na Tottenham da kuma na Wolverhampton da Newcastle United a 2010.

Ƴan wasan da aka bai wa katin gargaɗi:

Ƴan wasan Bournemouth

  • M. Senesi
  • A. Smith
  • R. Christie
  • L. Cook
  • J. Kluivert
  • A. Semenyo

Ƴan wasan Chelsea

  • Robert Sánchez
  • Marc Cucurella
  • L. Colwill
  • W. Fofana
  • Renato Veiga
  • N. Jackson
  • Joao Felix
  • Jadon Sancho