Valladolid ta kori mai horar da ita Cocca

Asalin hoton, Getty Images
Real Valladolid ta kori kociyanta, Diego Cocca bayan jan ragamar wasa takwas, kamar yadda ƙungiyar da ke buga La Liga ta sanar ranar Litinin.
Ƙungiyar tana ta karshen teburin La Liga na bana, bayan rashin nasara karo biyar a jere.
An bai wa Cocca aikin horar da Valladolid ranar 14 ga watan Disamba, kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar nan.
Sai dai wasa ɗaya ya ci daga takwas da ya ja ragama - an bai wa Alvaro Rubio aikin riƙon ƙwarya a karo na biyu.
Valladolid ta sha kashi a wasa shida a lik karkashin Cocca har da 4-0 a gida a hannun Sevilla ranar Lahadi.
Haka kuma ta yi ban kwana da Copa del Rey a zagayen ƴan 32 a hannun wata karamar ƙungiya mai buga gasar Sifaniya mai daraja ta uku, Ourense CF a watan jiya.
A watan Nuwamba Valladolid ta raba gari da Paulo Pezzolona, saboda rashin nasara 5-0 a gida a hannun Atletico Madrid, bayan cin wasa biyu daga 15 a lik a bana.
A lokacin ne ta bai wa Rubio aikin riƙon ƙwarya har sai da ta ɗauki Cocca.
A bara ne Valladolid ta samu gurbin da ta shiga La Liga karkashin Pezzolano - yanzu tana da maki 15 ta karshen teburi bayan wasannin mako na 24.
Valladolid za ta ziyarciAthletic Bilbao ranar Lahadi a wasan La Liga.











