Girke-girken Ramadan: Yadda ake abincin sadaka na farfesun naman akuya da burodi

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Girke-girken Ramadan, shiri ne da BBC Hausa take kawo muku tsawon kowane watan azumin Ramadan, don bai wa mutane damar gwangwaje basirarsu ta girki.

A wannan bidiyo - wanda shi ne na farko a wanna shekara - Raja'atu Muhammad, wadda aka fi sani da 'Diaryofnortehrcook a fashin Instagram, ta bayyana mana yadda ake haɗa abincin sadaka domin ciyar da mutane a lokacin azumi.

Abincin da ta girka a yau shi ne farfesun naman akuya da burodi da kuma Apple, domin raba wa mabuƙata don shan ruwa.