Zan ci gaba da yin takara har sai na zama gwamnan Kano - Sheikh Khalil

Bayanan bidiyo, Latsa lamar da ke sama domin kallo
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Ɗan takarar gwamnan Kano a jamʼiyyar ADC 2023, Malam Ibrahim Khalil ya ce zai ci gaba da yin takarar gwamna a jihar Kano har sai ya cimma burinsa.

Sheikh Khalil wanda ya taɓa yin takarar gwamnan Kano sau ɗaya da kuma takarar neman zama ɗan takara gwamna a baya, ya kasance cikin waɗanda suka fi samun ƙuri'u a zaɓen 2023, a bayan jam'iyyun NNPP da APC da kuma PDP.

''Mu, Kano da al'ummar Kano da ci gaban kano muke yi wa, da kuma kokarin ceto Kano daga inda ta samu kanta kuma ba za mu daina ba har sai mun ci nasara," kamar yadda ya shaida wa BBC.

Ya kuma ce yana da tabbacin cewa jam'iyyar ADC - wadda a yanzu ƴan hamayya suka yi hadaka a cikinta - za ta bayar da mamaki nan gaba, "matuƙar ba su tsaya masu sayar da jam'iyya sun sayar da su ba, ko su haifar da babbar rigima da za ta cire wa al'umma buri".

A cewarsa, mutane da yawa ko a jam'iyyar ADC ko ba a cikinta ba, na so a kayar da gwamnatin Bola Tinubu, sai dai ya ce "cire gwamnatin yanzu ba abu ne mai sauƙi ba."

A farkon watan Yuli ne dai manyan ƴan adawar siyasa na Najeriya suka dunƙule a jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin jam'iyyar da za su tunkari zaɓen 2027.

Hakan na zuwa ne bayan yunƙuri daban-daban da ƴan adawar suka yi na ganin sun samar da kyakkyawarar adawa da za ta iya kayar da gwamnatin shugaban ƙasar mai ci Bola Ahmed Tinubu, wanda suke zargi da gazawa a mulkinsa.

'Muna maraba da ƴan siyasa ADC'

Dangane kuma da sabbin ƴan siyasar da suka shiga jam'iyyar ADC ta haɗaka, Malam Ibrahim Khalil ya ce suna murna da maraba da manyan ƴan siyasar da suka shiga jamʼiyyar tasu domin ƙulla haɗaka.

'' Hakan na nuna cewa raina jamiyya, a ce ita ƙarama ce, duk ba haka ba ne, duk Jam'iyyu darajarsu ɗaya ce sai dai a ce wasu na da gwamnati wasu ba su da gwamnati''. In ji Sheikh Khalil.

A cewarsa duk lokacin da dansiyasa ya rasa mafaka, duk jam'iyyar da ya gani nan zai faɗa.

"Su wadannan da suka shigo an ɓata musu rai ne ko sun rasa buƙatarsu, a inda suka baro, kuma suka shigo ADC da baki ba da jikinsu ba, a ƙarshe suka ga ba inda yake mafi kyau da tsira sai ADC.

'Mu ƴan ADC ba abin da za mu yi sai dai mu godewa wa Allah, kuma wannan ci gaba ne ga jamiyyar'', in ji Malamin addinin.

Makomar ADC bayan zaɓen cikin gida

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To sai dai wasu ƴan Najeriya na hasashen jamiyyar ta ADC za ta iya tarwatsewa idan an zo fitar da ɗan takarar shugaban kasa, ganin cewa da dama daga cikin jiga-jigan da suka shige ta suna neman wannan matsayi ne.

Malam Ibrahim Khalil ya ce hakan zai iya yiwuwa, sai dai ya ce shi tsohon gwaman jihar Anambra, kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour wato Peter Obi har yanzu bai tsaya da kafarsa ba.

"Ya fi kama da yana nan a jamiyyarsa ta Labour, saboda har yanzu jaridun ƙasar na cewa yana so ya yi takarar shugaban kasa, ta biyu kuma ya faɗa ya ce idan ya shiga ADC yana so ya fara yin takarar amma shekara huɗu zai yi, don haka ba za a sa shi cikin lissafi ba,'' a cewar Malam Khalil.

Ya kuma ce dama ita jamiyyar haɗakar ta kasu kashi huɗu ne, kashi ɗaya an ma daina jin sa, ɗaya kuma shi ne inda Peter Obi ke ciki, shi kuma har yanzu yana kan katanga kafarsa biyu na jam'iyyar labour, kuma yadda yake son shugaba kasa, haka Atiku ke so.

Ya kamata a haɗa Atiku da Obi su yi takara a ADC

Wani abu da aka daɗe ana tambaya a kai shi ne, ko me ya sa manyan ƴan takara ba za su hakura su bai wa sabbin jini dama ba?.

A cewar malam Ibrahim, hakan ba zai yiwu ba ''saboda shi ɗan siyasa ba ya jin nasiha, baya jin shawara kuma ba ya jin bari, bukatarsa ce kawai a gabansa, ba ruwansa da abin da zai je ya dawo.'

Ɗan siyasar ya kuma ce da "jiga-jigan jam'iyyar za su iya, abin da ya kamata su yi shi ne su sa Atiku a matsayin shugaban ƙasa, Peter Obi ya yi masa mataimaki, sai a lalubo wani mai ƙarfi a cikinsu daga wani ɓangare ya yi sakataren gwamnati, da sun zauna, sai dai a cewar sa ''matsalar ƴan siyasa ba su da tunani mai faɗi''.

Tsohon ɗantakarar gwamnan a jam'iyyar ADC, ya kuma ce ba abin mamaki ba ne idan aka ce wasu mutane na shiga jam'iyyar domin su hana su zaman lafiya.

''In ma an yi ba wani abu ne sabo ba saboda babu wata gwamnati da za ta yarda a zo a kayar da ita''

Ra'ayinsa kan shugaba Tinubu

Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano a jamʼiyyar ADC 2023, Malam Ibrahim Khalil, ya ce Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu shi ne ya fi dacewa da ƴan siyasa da al'ummar Najeriya kasancewarsa "warki".

A wata hira da sashen Hausa na BBC, Malam Ibrahim Khalil ya kuma a ce a tarihi ba a taɓa yin gwamnatin siyasa da ta san abin da take yi ba, kuma ta yi maganin kowa da kowa kamar gwamnati mai ci a yanzu.

"Babu wani ɗan siyasa kamar Shugaban Najeriya Bola Tinubu da ya san abin da yake so kuma ya san yadda zai biya bukatarsa, 'shi ne ya fi dacewa da ƴan Najeriya da ƴan siyasar ƙasar.''