Matar da ta mutu bayan kwaikwayon yadda ake haihuwa a shafin YouTube

    • Marubuci, Xavier Selvakumar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wata mata a gundumar Tiruppur da ke jihar Tamil Nadu ta mutu bayan ta yi ƙoƙarin haihuwa a gida, ba tare da zuwa asibiti ko neman shawarar likita ba,.

Ta kalli bidiyon yadda ake haihuwa a gida a shafin YouTube sannan ta yi yunƙurin yin hakan, wanda a ƙarshe ya yi sanadiyar mutuwarta.

A halin yanzu, jaririyar da aka haifa tana jinya a asibiti. Kan batun da ta shafi mutuwar matar, an shigar da ƙara a kan mijinta. Sai dai ƴan sanda sun ce har yanzu ba a kama kowa kan wannan lamarin ba.

Wani bincike da hukumomin lafiya suka gudanar ya nuna cewa ma'auratan sun haifi ɗiya shekara shida da suka gabata ta hanyar tiyata. Don haka, wannan lokacin sun yanke shawarar matar za ta gwada haihuwa da kan ta. Hukumomin sun kuma ce ma'auratan ba su ɗauki wata shawara daga ƴan uwansu ba.

An kuma gano cewa wasu matan duk da suna sane da cewa akwai alluran rigakafi da magunguna, da tallafin da sashen kiwon lafiya ke bayarwa a cikin makonni 12 bayan haihuwa, ba sa amfana da waɗannan ayyukan.

Wata likitar haihuwa mai suna Geeta ta ce haihuwa a gida na iya jefa rayuwar uwa da jariri cikin hadari.

Ƙin zuwa asibitin da yunƙurin haihuwa a gida

Katti Sami mai shekaru 40 da matarsa ​​Shashikala ƴar shekara 32, waɗanda ke zaune a ƙauyen Punchai Thalavaipalayam kusa da Uthukuli a gundumar Tiruppur, dukkansu suna da digirin injiniyanci. Katti Sami manomi ce. Ma'auratan sun haifi diya ƴar shekara 6.

Shashikala ta sake yin ciki. Ta shiga naƙuda ne a ranar 23 ga watan Yuni kuma ta haihu a gida. Bayan haihuwa, lafiyarta ta taɓarɓare kuma an kwantar da ita a wani asibiti mai zaman kansa a Coimbatore. Ta rasu a can ranar 28 ga watan Yuni.

Sakamakon ƙorafin da ma'aikatar lafiya ta shigar, ofishin ƴan sanda na Uthukuli ya shigar da kara a kan lamarin.

A cewar ƴan sandan Uthukuli, mijin da matar sun amsa cewa sun yanke shawarar haihuwa a gida da kansu, ba tare da neman wata shawara ko taimako daga ƴan uwansu ba.

A cewar ƴan sanda, da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar 23 ga watan Yuni, mijin Shashikala shi kaɗai ya shirya karɓar haihuwar a lokacin da yake kallon wani bidiyo a YouTube. Washe gari aka haifi ɗiya mace. Bayan an haihu, Shashikala ta sha fama da matsanancin zubar jini kuma ta rasa hayyacinta. Daga nan aka garzaya da ita wani asibiti mai zaman kansa da ke kusa, inda aka ba ta kulawar gaggawa, sannan aka miƙa ta asibitin kwalejin kiwon lafiyar Jama'a na gwamnati da ke Perundurai.

Lokacin da yanayin jikin na ta ya tsananta, likitoci sun ba da shawarar a kai ta asibitin kwalejin kiwon lafiyar Jama'a na gwamnati da ke Coimbatore. Amma sai danginta su ka kai ta wani asibiti mai zaman kansa a Coimbatore.

Ta rasu ne yayin da ta ke jinya a can ranar 28 ga watan Yuni. Ma'aikatar lafiya ta ce har yanzu ana ci gaba da kula da jaririyar a asibitin kwalejin kiwon lafiyar Jama'a da ke Perundurai.

Shashikala da mijinta sun yi aure a ranar 23 ga Fabrairu, 2019. A shekara guda bayan nan, sun haifi ƴarsu ta fari, wadda aka haifa ta hanyar tiyata. A cewar sanarwar da ƴan sanda suka fitar, mijin nata ya bayyana cewa saboda wasu dalilai, Shashikala ta yanke shawarar haihuwa a gida.

A lokacin da ta ke da ciki na biyu, Shashikala ba ta ma je asibiti domin a duba lafiyarta ba. Ƴan sandan sun ce ta riga ta shaida wa surukarta da ƙanwarta da iyayenta cewa za ta haihu a gida. Ma'aikatar lafiya ta kuma tabbatar da wannan bayanin.

Haihuwa a gida na iya sanya rayuwar uwa da jariri cikin haɗari!

Dokta Geeta ita ce Shugabar Sashen kula da mata masu juna biyu a asibitin kwalejin kiwon lafiya na Gwamnati a Coimbatore. Ta yi bayanin illolin da ke tattare da lafiyar jiki kafin haihuwa da kuma lokacin haihuwa, ta kuma yi bayani dalla-dalla kan dalilin da ya sa haihuwar mace a gida ya fi hatsari kan idan ta je asibiti.

Da take magana da BBC, Dr. Geeta ta ce: "Gaba ɗaya, matsaloli daban-daban na iya tasowa yayin haihuwa, yayin da mace ke da juna biyu, haɗarin kamuwa da hawan jini, da rashin jini a jiki, da ciwon sukari. Don haka, kowane wata muna duba hawan jini, matakin sukari na jini da matakin sinadarin haemoglobin na mata masu ciki. Idan an gano waɗannan matsalolin da wuri, za mu iya magance su yadda ya kamata."

Ta ƙara da cewa: "Idan ba a gano waɗannan cututtuka ba, yana da wuya a iya hasashen yadda haihuwa za ta kasance, idan ba a iya kula da yanayin wurin da ake haihuwan ba, za su iya haifar da matsaloli masu tsanani, yayin haihuwa, yana da muhimmanci a sau cewa jikin mace ya buɗe yadda ya kamata domin taƙaita zubar jini. Ana yin haka ta hanyar aikin likitanci mai suna 'Active Management of the Third Stage of Labour' (AMTSL), wanda ake gudanar da shi tare da allurai da magunguna na musamman, kuma a asiiti kawai ake iya yin su.''

Alamu sun nuna cewa marigayiyar ta taɓa haihuwa ta hanyar tiyata a baya. Idan mace ta taɓa haihuwa ta hanyar tiyata, za ta iya fuskantar matsaloli idan ta nemi ta haihu da kanta bayan nan.

Dr. Geeta ta ce: "Idan mace ta taɓa haihuwa ta hanyar tiyata, za a iya samun ƙalubale da dama yayin haihuwa ta gaba. Akwai wuraren da aka yi wa ɗinki a ciki da kuma mahaifa. Waɗannan wuraren dinkin na iya tsagewa, har ma mahaifar kanta ta iya samun tsagewa. Idan hakan ya faru, zai yi matuƙar wahala a ceto rayuwar uwar da jaririn. Amma idan suna asibiti, za a iya sa ido sosai kan yanayinsu tare da ba su kulawar da ta dace."

Ta ƙara da cewa: "Kamar yadda wanda zai iya tuƙa ƙaramar mota ba yana nufin zai iya tuƙa babbar mota, haka nan, wanda ke kallon bidiyon YouTube ba yana nufin zai iya haihuwa a gida kuma ya iya yi cikin sauƙi. A yau akwai mutane da dama waɗanda suka yi imanin cewa haihuwa da kansu(ba tare da tiyata ba) ita ce mafi kyau, amma hakan ba koyaushe ya ke zama gaskiya ba. Sai lokacin da uwa take da lafiya ne kawai zai yiwu a haifi jariri mai lafiya," in ji Dr. Geeta, likita mai ƙwarewa a fannin haihuwa.