Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da gaske sojojin Najeriya sama da 100 sun tsere da makamansu a Borno?
Masana tsaro a Najeriya na ci gaba da tsokaci kan yadda wasu jami'an sojin Najeriya sama da 100 suka tsere da makamansu, yayin wani hari da mayaƙan ISWAP suka kai kan Bataliya ta 162 da ke jihar Borno.
Rundunar sojin Najeriyar dai ta ce lamarin ya faru ne tun ranar 5 ga watan Yunin 2026, lokacin da mayaƙan na ISWAP suka kai hari kan sansanin da ke kan hanyar Mandara zuwa Buratai a ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno, inda suka kashe sojoji guda biyar.
A cewar wata takardar cikin gida da ta ɓulla daa rundunar, harin ya faru ne da misalin ƙarfe huɗu na asuba a lokacin da ake zabga ruwan sama mai ƙarfi, abin da ake ganin ya rage wa dakarun damar hango maharan cikin lokaci sa'ad da suka tunkaro su.
Bayan faruwar harin ne, rundunar ta ce ta gudanar da ƙididdigar dakarunta, inda ta gano cewa sojoji 104 sun ɓace daga sansanin kuma ba su dawo bakin aikinsu ba.
Rundunar ta ce sojojin sun tafi ne da makamansu, lamarin da ya sa aka ayyana su a matsayin wadanda suka tsere daga fagen daga, tare da umartar dukkan rundunonin soji da hukumomin tsaro su cafke su a duk inda aka gansu.
Takardar ta kuma nuna cewa cikin sojojin da aka ayyana akwai jami'i guda ɗaya mai muƙamin Staff Sajan, da Sajan uku, da Kofur bakwai, da Laskofur 38 da kuma sauran ƙananan jami'ai 55.
Haka kuma an ba da umarnin dakatar da albashinsu da sauran haƙƙoƙinsu har sai an kammala bincike kan lamarin.
An ruwaito cewa harin ya yi sanadin mutuwar wasu sojoji da kuma mambobin ƙungiyar ’yan sa-kai na farar hula da ake kira Civilian JTF, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
Sai dai babu wata shaida da ke nuna cewa sojojin da suka yi ɓatan dabo sun faɗa hannun mayaƙan na ISWAP ko kuma sun haɗa kai da su.
''Ba ƙaramin abun tashin hankali bane''
A cewar wani masananin harkokin tsaro a Najeriya Captain Sadiq Abubakar mai ritaya, bacewar sojoji sama da 100 tare da makamansu babban ƙalubale ne ga rundunar sojin Najeriya.
Ya ce laifin guduwa daga aiki na daga cikin manyan laifukan soja, kuma dokokin rundunar sun tanadi hukunci mai tsauri ga duk wanda aka samu da laifin idan kotun soja ta same shi da laifi.
Sai dai ayyana soja a matsayin wanda ya tsere daga fagen daga ba wai yana nufin an same shi da laifi ba ne, domin ana iya gudanar da bincike da kuma shari'a idan aka kama shi.
Ya kara da cewa raguwar yawan dakarun a fagen daga matsala ce, sai dai wata ƙarin matsalar ita ce kasancewar sun tafi ne da makamansu, don haka akwai yiwuwar amfani da su ta hanyoyin da ba su kamata ba.
Lamarin ya kuma sake jawo hankali kan irin matsin lambar da dakarun da ke fafatawa da ƙungiyoyin ISWAP da Boko Haram ke fuskanta, musamman a yankin tafkin Chadi da dazukan Sambisa da Mandara, inda hare-haren mayaƙan suka sake ƙaruwa cikin watannin baya-bayan nan.
A cikin 'yan shekarun nan, masana tsaro sun sha bayyana cewa mayaƙan ISWAP sun sauya dabarunsu, inda suke kai hare-hare kan sansanonin soji domin ƙwace makamai da motocin yaƙi, maimakon kai hari kan fararen hula kaɗai.
Ko da yake gwamnatin Najeriya ta sha bayyana cewa ta raunana Boko Haram da ISWAP, hare-haren da ake kai wa sansanonin soji da ƙauyuka a jihohin Borno, Yobe na ci gaba da tayar da hankali.
A cikin watannin baya-bayan nan an samu rahotannin hare-hare kan sansanonin soji da dama, inda aka kashe wasu dakaru, wasu suka jikkata, sannan aka lalata ko aka ƙwace wasu kayan aikin soja.
Masana na cewa hare-haren na nuna cewa har yanzu mayaƙan na da ƙarfin kai farmaki a wasu yankunan arewa maso gabashin Najeriya, duk da matsin lambar da suke fuskanta daga rundunar soji.