Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Jana’izar Khamenei da sauran abubuwan da ke faruwa a duniya 04/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwa kan Jana’izar Khamenei da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 4 ga watan Yulin 2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. Houthi ta yi barazanar kai hari kan filayen jiragen sama a Saudiyya

    Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta yi barazanar kai hare-hare kan filayen jiragen sama da sauran muhimman wurare a Saudiyya idan Riyadh ta ci gaba da abin da ta kira ƙeta sararin samaniyar Yemen.

    Kakakin rundunar Houthi, Yahya Saree, ya ce mayaƙansu sun fuskanci jiragen yaƙin Saudiyya da suka yi ƙoƙarin hana wani jirgin saman farar hula na Iran sauka a filin jirgin saman Sanaa.

    Ya kuma jaddada cewa zirga-zirgar jirage tsakanin Sanaa da Tehran za ta ci gaba.

    Tashar Al-Masirah mai alaƙa da Houthi ta ruwaito cewa wani jirgin Iran ya isa Sanaa a ranar Juma’a ɗauke da wakilan ƙungiyar da suka halarci jana'izar tsohon jagoran Iran, Ali Khamenei, tare da sama da marasa lafiya 200.

    A martaninta, ƙawancen sojojin da Saudiyya ke jagoranta ya ce kalaman Houthi wani yunƙuri ne na kau da hankali daga abin da ya kira ayyukan ƙungiyar a Yemen, tare da yin gargaɗin cewa zai mayar da martani mai ƙarfin da ba a taɓa gani ba ga duk wani hari kan Saudiyya.

  2. 'Sama da ƴan gudun hijira 640,000 sun koma gidajensu a Lebanon'

    Ƙungiyar Kula da Ƙaura ta Duniya (IOM) ta bayyana cewa sama da mutum 640,000 da rikicin ya raba da muhallansu a Lebanon sun koma gidajensu bayan raguwar faɗace-faɗace da kuma yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Sai dai ƙungiyar ta ce har yanzu kusan mutum 500,000 na ci gaba da ƙaura, ba tare da sun samu damar komawa gidajensu ba.

    Rahoton ya dogara ne kan bayanan da aka tattara tun daga ranar 22 ga watan Yuni tare da haɗin gwiwar hukumomin yankin.

    Lebanon ta faɗa cikin rikicin yankin a farkon watan Maris lokacin da ƙungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Tehran ta harba makamai masu linzami zuwa Isra'ila, bayan kashe jagoranaddinin Iran a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra'ila.

    A martaninta, Isra'ila ta ƙaddamar da hare-haren sama da kuma farmaki ta ƙasa a kudancin Lebanon.

    Jami'an Lebanon sun ce hare-haren Isra'ila sun kashe kusan mutum 4,300 tare da raba fiye da mutum miliyan ɗaya da gidajensu, musamman a kudancin ƙasar da kuma kudancin unguwannin Beirut.

  3. Za a yi wa gawar Khamenei sallar jana'iza ranar Lahadi

    Mahukuntan Iran sun sanar da cewa za a yi wa gawar Ayatollah Ali Khamenei sallar jana'iza da safiyar Lahadi a harabar Mosalla da ke birnin Tehran.

    A cewar sanarwar da kafafen yaɗa labarai na Iran suka wallafa, za a gudanar da sallar ne da ƙarfe shida na safe, a wani ɓangare na bukukuwan jana'izar da ake yi wa tsohon jagoran addinin ƙasar.

    Sai dai sanarwar ba ta bayyana sunan wanda zai jagoranci sallar jana'izar ba.

    A halin yanzu ana ci gaba da zaman makoki da bukukuwan jana'izar Khamenei, waɗanda aka tsara za su gudana na tsawon kwanaki shida tare da halartar dubban masu makoki daga sassa daban-daban.

  4. Magoya bayan Ali Khamenei na kiran ɗaukar fansa

    Dubban magoya bayan Ayatollah Ali Khamenei sun taru a harabar Mosalla da ke Tehran, inda suka rika kiran a ɗauki fansa yayin da aka fara jana'izarsa.

    A cewar AFP, wasu daga cikin mahalartan sun ɗaga jajayen tutoci da alluna masu ɗauke da saƙonnin kira ga ɗaukar fansa, tun kafin isowar akwatin gawarsa wurin taron.

    Rahotanni sun ce masu makokin sun rika rera taken “Mutuwa ga Amurka” da kuma “Ramuwar gayya, ramuwar gayya”, suna bayyana buƙatar mayar da martani.

    Jana'izar, wadda aka shirya za ta gudana na tsawon kwanaki shida, ta kuma samu halartar manyan jami'ai da wakilai daga ƙasashen yankin, yayin da mahukuntan Iran ke sa ran miliyoyin mutane za su shiga cikin bukukuwan makokin da za a gudanar a Iran da Iraq.

  5. An Fara Jana'izar Ayatollah Khamenei a Birnin Tehran

    Dubban masu makoki ne suka taru a yankin Mosalla da ke birnin Tehran domin halartar jana'izar Ayatollah Ali Khamenei, tsohon jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

    An buɗe ƙofofin arewacin harabar Mosalla ga jama'a da safiyar Asabar, inda aka ajiye akwatin gawarsa domin mutane su yi masa bankwana na ƙarshe.

    Mahukuntan Iran sun ce an shirya zaman makoki da jana'izar na tsawon kwanaki shida, tare da hasashen cewa tsakanin mutum miliyan 15 zuwa 20 ne za su halarci bukukuwan da za a gudanar a birane daban-daban na Iran da Iraq.

    Wakilin kamfanin dillancin labaran AFP ya ce dubban mutane sun cika harabar Mosalla tun kafin isowar akwatin gawar, yayin da manyan jami'ai da wakilai daga sassa daban-daban na yankin suka halarci jana'izar.

    Ana sa ran bukukuwan za su jawo hankalin miliyoyin mutane a kwanaki masu zuwa yayin da ake ci gaba da gudanar da zaman makokin tsohon jagoran na Iran.

  6. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da wannan safiya ta ranar Asabar.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.