An tuhumi Arsenal da kasa tsawatar wa ƴan wasanta

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon kafa ta Ingila ta tuhumi Arsenal da kasa tsawatar wa ƴan wasa, bayan da suka mamaye alkalin wasa Michael Oliver, saboda jan katin da ya yi wa Myles Lewis-Skelly.

Lamarin ya faru ranar Asabar a wasan mako na 23 a Premier League da Gunners ta ci 1-0 a Wolverhampton a Molinuex.

Oliver ya bai wa Lewis Skelly jan kati kai tsaye, bayan da matashin ya yi wa Matt Doherty keta, inda alkalin wasan ya ce ya yi ne da mugun nufi.

Arsenal ta ɗauka kara kan hukuncin da aka yi wa mai shekara 18, wanda aka ce ba zai yi karawa uku ba, yanzu an soke jan katin.

An bai wa Arsenal nan da ranar 3 ga watan Fabrairu, domin ta kare kanta.

Ƴansanda na binciken barazana da cin zarafin da aka yi wa alkalin wasa Oliver a kafar sada zumunta.

Ranar Lahadi 2 ga watan Fabrairu Arsenal za ta karɓi bakuncin Manchester City a wasan mako na 24 a Premier League da za su kara a Emirates.

Arsenal tana mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 47 da tazarar shida tsakani da City, wadda take ta huɗun teburi.